Muhammad Ahamed | Katsina Times
Wani mummunan lamari ya auku a garin Uromi, Jihar Edo, inda wasu fusatattun jama’a suka halaka matafiya 16 daga Arewa bisa zargin 'yan ta'adda ne.
Lamarin ya faru ne bayan wata kungiyar sa-kai ta tsayar da motar da ke dauke da matafiyan daga Fatakwal zuwa Kano domin bikin Sallah.
Rahotanni sun nuna cewa an samu makamai irin su adduna da bindigogi na gargajiya (dane guns) a hannun su, wanda ya tayar da hankulan jama’a, har suka yi zargin cewa su barayi ne. Matasa suka yi wa matafiyan taron dangi, duk da kokarin su na kare kansu.
“Sun roka, suna cewa matafiya ne na Sallah, amma babu wanda ya saurare su,” in ji wani ganau. “Har wani daga cikinsu aka tura da kafa cikin wutar da aka kunna.”
Yayin da jami’an tsaro suka iso wurin, mutum 12 sun riga da sun mutu, an kuma kona gawarwakinsu. Mutum hudu kacal aka tsinto da rai, amma cikin munanan raunuka.