Kungiyar ISMA Medical Care Initiative, reshen kula da lafiya na Harkar Musulunci a Katsina, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar cizon sauro (Malaria) domin fadakar da al’umma game da hadurranta da hanyoyin kariya.
Wakilin bangaren ISMA, Mallam Dauda Lawal, ne ya jagoranci taron wanda aka gabatar a yau, Asabar, 22 ga watan Ramadan, a muhallin Tafsirin Ramadan. Ya yi bayani dalla-dalla kan yadda cutar ke yaduwa, hanyoyin kariya da rigakafi, da kuma illolinta ga rayuwar al’umma.
A cikin jawabinsa, Mallam Dauda ya jaddada cewa inganta tsaftar muhalli na daga cikin matakan dakile yaduwar sauro da cutar cizon sauro. Ya bayyana cewa hana ruwa zama a kwatoci da magudanan ruwa (drainages) zai hana samuwar muhalli mai kyau ga sauro. Haka nan, sanya shara a cikin manyan ledoji da rufe bokitin shara na cikin gida na taimakawa wajen dakile yaduwar sauro.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika amfani da gidan sauro, tare da kai yara asibiti domin karbar rigakafin cututtuka da suka hada da zazzabin cizon sauro. Har ila yau, ya gargadi mutane da su guji shan magunguna barkatai ba tare da izinin likita ba, yana mai jaddada cewa neman magani da wuri a asibiti yana da matukar muhimmanci wajen rage hadurran cutar.
A karshe, Mallam Yakubu Yahya ya rufe taron da addu’o’in fatan Allah Ya kare al’umma daga cututtuka da kuma sharrin azzaluman mahukunta.