INEC ta karbi takardar neman yi wa Sanata Natasha kiranye

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24032025_153138_FB_IMG_1742824111615.jpg


Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta karɓi ƙorafi da ke neman fara yunƙurin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye a matsayin Sanata.

Sakataren hukumar, Rose Oriaran-Anthony ce, ta karɓi ƙorafin a yau Litinin.

Ƴan mazaɓar, a wata wasika da jagoran su, Salihu Habib ya sanyawa hannu, sun nuna cewa sun dawo daga rakiyar wakilcin Natasha a majalisar dattawa.

Masu korafin, karkashin ƙungiyar Concerned Kogi Youth and Women, sun yi kira ga INEC da ta gaggauta sahale yunƙurin kiranyen, wanda su ka ce hakan hakan na da kyau wajen karfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Hakan ya zo ne bayan da tun a farko, kotu ta hana INEC karɓar korafi na yunkurin yi wa Natasha kiranye, amma kuma wanne tudu wanne gangare, sai kotun a yau Litinin ta baiwa hukumar zaben damar karbar korafe-korafen.

Follow Us