Matasa Sun Fara Gwada Karfin Su a Siyasa: Tawagar Salman Gafai Ta Ziyarci Ofishin SDP a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19032025_233635_FB_IMG_1742427329015.jpg



A kokarin kafa sabon shafi a siyasar matasa a jihar Katsina, tawagar matasa karkashin jagorancin matashin dan siyasa, Salman Ahamed Gafai, sun kai ziyara zuwa ofishin jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) domin jaddada cikakken goyon bayansu ga tafiyar jam'iyyar.

A lokacin ziyarar, sakataren jam'iyyar SDP a jihar Katsina, Mustapha Kurfi, ya tarbi tawagar matasan a madadin shugaban jam'iyyar, Bello Safana.

Da yake jawabi, Salman Gafai ya bayyana cewa matasan sun dauki wannan mataki ne domin nuna rashin gamsuwa da manufofin jam’iyyar APC a matakin jagorancin kasa. Ya ce:

"Mu matasa ne masu kishin al'umma, kuma muna da hakkin mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da shugabanci nagari. Duk wata tafiya da ba ta kare muradun al'umma ba, ba za mu mara mata baya ba. Mun zo nan ne domin bayyana cewa muna cikin tafiyar SDP dari bisa dari, domin muna ganin ita ce tafiyar da za ta kawo ci gaba mai dorewa ga matasa da al’umma gaba daya."

Sakataren jam’iyyar SDP, Mustapha Kurfi, tare da shugaban matasan jam’iyyar, Mustapha Abdullahi, sun nuna gamsuwa da yadda matasa ke karbar jam’iyyar. Sun bayyana cewa wannan karuwar matasa a tafiyar SDP alama ce ta nasarar da jam’iyyar ke samu a jihar.

A cikin tawagar da suka raka Salman Gafai zuwa ofishin SDP sun hada da: Abas Usman, Mubarak Abdullahi, Ana’s Kabir, Tasiu Nafiu Kabir, da Abdullahi Ibrahim.

Wannan ziyara tana daga cikin ci gaban yunkurin matasa na shiga harkokin siyasa don taka rawar gani a tsarin shugabanci na kasa.

Follow Us