"Dalilin da Ya Sa Na Boye Alburusai Cikin Jarkar Man Ja" – Wacce Ake Zargi da Safarar Makamai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19032025_143416__114750571_police.jpg.webp



Katsina Times 

Wata mata da ake zargi da safarar makamai, Hauwa Sani, ta amsa laifin ɓoye harsasai 124 a cikin jarkar man ja domin isar da su ga ‘yan bindiga cikin sauki.

An kama Hauwa, wadda ta yo safarar  makamai da kuma fataucin miyagun kwayoyi, a kan babbar hanyar Keffi-Abuja ta hannun jami’an Rundunar Musamman ta ‘Yan Sanda. A yayin bincike, ta bayyana cewa wani mutum mai suna Nasiru daga Daura ne ya ba ta umarnin kai harsasan zuwa Jihar Katsina.

Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Abuja a ranar Talata, Kakakin Rundunar, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Olumuyiwa Adejobi, ya bukaci ‘yan kasa da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargin na da alaka da aikata laifi ga hukumomin tsaro.

“Ya zama dole jama’a su kasance masu fahimtar dabarun da masu safarar makamai ke amfani da su. Duk wani abu da ake zargi ya kamata a kai rahotonsa ga hukumomin da suka dace,” in ji Adejobi.

Ya kara da cewa binciken da rundunar ta gudanar ya kai ga ƙarin kama wasu mutane da kuma samun wasu kayayyakin haramtattu, wanda ake ci gaba da bincike a kansu. Ya tabbatar da aniyar rundunar wajen dakile ayyukan masu laifi, ciki har da safarar makamai, fataucin miyagun kwayoyi da kuma jabun kuɗi.

“Wadannan nasarori sun nuna jajircewar tawagoginmu na musamman, musamman ma Rundunar Bincike ta Musamman ta Sashen Leken Asiri (FID-STS),” in ji shi.

A wani samame da aka gudanar a ranar 1 ga Fabrairu, 2025, jami’an FID-STS, bisa sahihan bayanan sirri, sun kama wasu mutum uku da ake zargi—Alhaji Usman Yahaya, mai shekara 50; Joseph Matthew, mai shekara 27; da kuma Solomon Bala, mai shekara 25—dukkaninsu mazauna Potiskum, Jihar Yobe.

Follow Us