Gwamna Fubara, Mataimakinsa da ‘Yan Majalisa Sun Shiga Dakatarwa
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 18 Ga Maris 2025
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokoki na jihar har tsawon watanni shida.
Shugaban kasar ya bayyana haka a wani jawabi da ya yi ga ‘yan Najeriya, da yammacin ranar Talata, yana mai cewa rikicin siyasar da ke ci gaba da dagule al’amura a jihar ya kai wani mataki mai tayar da hankali, wanda ke barazana ga zaman lafiya da dimokuradiyya.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tun bayan fara rikicin siyasar Jihar Rivers, al’ummar jihar sun rasa damar cin gajiyar mulkin dimokuradiyya saboda rikicin ya hana gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Ya ce, Gwamna Fubara ya rushe ginin Majalisar Dokoki tun a ranar 13 ga Disamba, 2023, kuma har yanzu bai sake gina shi ba. Duk da kokarin da shugabanni da kungiyoyin kasa suka yi don warware rikicin, babu wata nasara da aka cimma.
Shugaban kasa ya kuma yi nuni da hukuncin Kotun Koli na ranar 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya bayyana cewa babu gwamnati mai cikakken iko a jihar, saboda an hana Majalisar Dokoki aiki. Kotun ta ce:
"Ba za a iya cewa gwamnati na wanzuwa ba idan ɗaya daga cikin rassanta uku ba ya aiki. A wannan yanayin, shugaban bangaren zartaswa ya hana bangaren dokoki aiki don ya tafiyar da mulki kamar mai mulkin kama karya. Don haka, babu gwamnati a Jihar Rivers."
Bayan nazari da bitar halin da ake ciki, Shugaba Tinubu ya ce ya zama dole ya yi amfani da Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya don ayyana dokar ta-baci a jihar daga ranar 18 ga Maris, 2025.
Saboda haka, an dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki har tsawon watanni shida. Shugaban kasa ya kuma nada tsohon Hafsan Sojan Ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (Rtd), a matsayin mai rikon mukamin gwamnan jihar.
Ya bayyana cewa dokar ta-baci ba za ta shafi bangaren shari’a ba, domin kotuna za su ci gaba da aiki kamar yadda doka ta tanada. Haka nan, sabon mai rikon mukami ba zai kirkiri sabbin dokoki ba, amma zai iya tsara ka’idoji na gudanar da ayyuka, bisa amincewar Majalisar Zartaswa ta Tarayya da shugaban kasa.
Shugaban kasa ya bayyana cewa wannan mataki na tilas ne don tabbatar da doka da oda, tare da dawo da dimokuradiyya a jihar. Ya ce an riga an wallafa sanarwar dokar ta-bacin a Jaridar Gwamnati kuma an aika da ita zuwa ga Majalisar Dokoki ta Tarayya.
A karshe, Shugaba Tinubu ya yi fatan wannan mataki zai kawo zaman lafiya da daidaito a Jihar Rivers, tare da tabbatar da biyayya ga doka da tsarin mulki a fadin Najeriya.