Kansilolin Kankara Sun Yi Zargin Sanya Hannu Na Bogi a Kasafin Kuɗi


Shugaban Karamar Hukuma Ya Musanta Zargin

Wasu kansilolin da aka zaɓa a Karamar Hukumar Kankara ta jihar Katsina, sun yi zargin cewa sa hannun da aka haɗa a kasafin kuɗin da aka kai Majalisar Dokokin Jihar Katsina ba nasu ba ne. Sun ce ba a tuntube su ba kafin a tsara kasafin, don haka bai wakiltar mazabun da suke wakilta ba.

Kansilolin sun zargi Shugaban Karamar Hukuma, Anas Isah, da shirya kasafin tare da wasu mutane da ba su da hurumin yin haka. Sun bayyana cewa an kira su zuwa gidan gwamnati, daga nan kuma aka ce su wuce majalisa don gabatar da kasafin. Amma sai suka ga an gabatar da wani lissafi da ba su da masaniya a kansa, kuma aka haɗa wata takarda da ke nuna cewa wai su ne suka sanya hannu.

A wata hira da Katsina Times, kansilolin da suka yi korafi sun tabbatar da cewa basu da masaniya kan abubuwan da kasafin kuɗin ya ƙunsa kafin a gabatar da shi.

Shugaban Karamar Hukuma Ya Mayar Da Martani

Da Katsina Times ta tuntubi Shugaban Karamar Hukumar Kankara, Anas Isah, ya musanta zargin. Ya ce kasafin kuɗin an tsara shi da sanin kowa, kuma idan akwai shakku kan sa hannu, a duba takardun da kansilolin suka sanya hannu a baya a kwatanta.

Ya ce:

"Ni ba ni ne shugaban karamar hukuma a watannin baya ba. Me zai sa in yi wa wani kansila karya kan sa hannu?"

Sannan, clerk na karamar hukumar, Abdulhadi Fayo, ya tabbatar da cewa kansilolin sun sanya hannu kan kasafin kuɗin. Ya ƙara da cewa:

"Za a iya zuwa ofishina a duba takardun da suka rattaba hannu don a ga ko akwai bambanci."

Lokacin da aka tambaye shi ko kansilolin sun bada gudunmawa wajen tsara kasafin, ya ce:

"Wannan tambaya ya kamata a yi wa shugaban karamar hukuma."

Dan Majalisa Ya Tabbatar da Matsalar da Aka Samu

Daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar, wanda ke cikin kwamitin tantance kasafin kuɗin kananan hukumomi, ya shaida wa Katsina Times cewa lallai akwai matsala a kasafin Karamar Hukumar Kankara.

Ya ce:

"Ranar da aka kawo kasafin, wani kansila mai suna Saifullahi Mato ya yi korafi sosai, amma sai aka ce shi ba zababben kansila ba ne, don haka ba lallai ne a tuntube shi ba."

Ya bayyana cewa kasafin ya zo da wasu kura-kurai, har ta kai ga ba a karɓe shi a ranar da aka gabatar da shi ba. Sun bukaci a gyara shi saboda ya yi kama da wanda aka kwafo daga wani tsohon kasafi don kawai a gabatar da shi cikin gaggawa.

Game da zargin sanya hannu na bogi, dan majalisar ya ce an kawo wannan korafi, amma a lokacin ba a ba shi muhimmanci sosai ba.

Shin Za a Sake Duba Kasafin Kuɗin Kankara?

Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina ta amince da kasafin kuɗin dukkanin kananan hukumomin jihar. Sai dai ana ci gaba da tambaya ko za a yi wani mataki dangane da korafin kansilolin Kankara, wadanda ke ganin ba a ba su damar jin ra’ayin jama’arsu kafin a tsara kasafin kuɗin.

Katsina Times

www.katsinatimes.com
Da sauran shafukan sada zumunta.

Follow Us