Kwamitin Sa Ido Ya Ziyarci Ayyukan Gyaran Gidajen Ruwa Don Samar da Tsabtataccen Ruwan Sha a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12032025_223047_FB_IMG_1741818535717.jpg




Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A ranar Laraba, 12 ga watan Maris, 2025, kwamitin sa ido kan ayyukan samar da ruwan sha a karkashin shirin NG-SURWASH, tare da rakiyar ‘yan jarida, ya ziyarci manyan gidajen ruwa guda bakwai a cikin birnin Katsina don duba yadda aikin gyara da fadada su ke gudana.

Kwamitin, karkashin jagorancin Muhammad Yusuf Sudais, ya duba yadda ake aiwatar da gyaran gidajen ruwa da ke Tudun ‘Yallihidda/Yammawa, Dutsin Safe Locust, Rahamawa/Abattoir, Sabuwar Unguwa/Janbango, Barhim Housing Estate, Barhim Bayan NYSC Camp, da Makera Housing Estate. Wadannan gidajen ruwa an gina su tun zamanin tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim Shehu Shema, fiye da shekaru goma da suka gabata. A halin yanzu, Gwamnatin Jihar Katsina, tare da Ma’aikatar Ruwa ta Jihar Katsina, na aiwatar da aikin gyara da sabunta su a karkashin shirin Bankin Duniya NG-SURWASH, wanda ke da burin tabbatar da wadatar tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.

Aikin gyaran gidajen ruwan na kunshe da:

Sake fasalin su zuwa tsarin zamani.

Shigar da na’urorin Solar Panel domin samun wutar lantarki daga hasken rana.

Fadada tsarin rarraba ruwa zuwa wasu unguwanni da ke makwabtaka da su.

Karin sabbin tankunan ruwa domin inganta wadatar ruwan.

Bayan ziyarar, kwamitin ya tattauna da jama’a domin jin ra’ayinsu kan aikin. Al’ummomin yankunan da aka zaga sun nuna matukar jin dadinsu, tare da alkawarta kula da wadannan wuraren domin tabbatar da dorewar ayyukan.

Wani mazaunin unguwar Dutsin Safe, da muka tattauna da shi, ya bayyana cewa:
"A baya muna samun ruwa, amma yawanci muna fama da karancin sa, musamman idan rijiyoyin sun tsaya ko kuma man Diesel da ake amfani da shi ya yi tsada. Amma yanzu, da wannan sabon gyara, muna da karin tankuna daga guda daya zuwa uku. Haka kuma an saka mana Solar Panel, wanda zai tabbatar da ci gaba da samar da ruwa ba tare da dogaro da dizal ba. Wannan na nufin ba mu kadai ba, har ma da unguwannin da ke kusa za su amfana."

Baya ga birnin Katsina, shirin NG-SURWASH na ci gaba da fadada ayyukan samar da tsaftataccen ruwan sha a dukkan kananan hukumomin jihar Katsina guda 34. Idan aikin ya kammala, ana sa ran Katsina za ta zama daya daga cikin jihohin da suka fi ci gaba wajen shawo kan matsalar ruwan sha a Najeriya.

Za mu ci gaba da bibiyar wannan ci gaba tare da kawo muku cikakken bidiyo da karin bayani kan yadda aikin ke gudana.

Follow Us