Sani Aliyu Dan Lami Ya Raba Shinkafa Dubu Uku Da Dari Uku Ga Al’ummar Karamar Hukumar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09032025_215854_FB_IMG_1741557337167.jpg

Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times

A wani yunkuri na tallafa wa al’umma a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Katsina, Hon. Sani Aliyu Dan Lami, ya raba buhunan shinkafa dubu uku da dari uku ga mazauna yankin.

An gudanar da bikin rabon kayan tallafin ne a ranar Lahadi, 9 ga Maris, 2025, a filin wasa na Pragon, da ke bayan dakin saukar baki na Alhayyat, cikin garin Katsina.

Taron ya samu halartar manyan baki, ciki har da Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Hon. Abdulkadir Nasir Andaje; Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa; Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Katsina, Hon. Ali Abu Albaba; Zababben Shugaban Karamar Hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad Ad Saude; da Babban Limamin Masallacin Juma’a na Kofar Soro, da sauransu.

A jawabin da ya gabatar, Hon. Dan Lami ya bayyana cewa manufar rabon tallafin ita ce rage radadin rayuwa ga jama’a a wannan lokaci, tare da tabbatar da ci gaba da irin wadannan shirin jin ƙai. Ya ce kimanin mutane dubu uku da dari uku ne suka ci gajiyar wannan tallafi, kuma akwai shirye-shiryen ƙarin tallafi da za a aiwatar a nan gaba domin inganta walwalar al’umma.

Mahalarta taron sun yaba da wannan kokari na Hon. Dan Lami, tare da yi masa fatan alheri a kan wannan hidima ta taimakon jama’a.

Follow Us