Hadimin Dan Majalisar Musawa/Matazu Ya Ajiye Aikinsa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08032025_124031_IMG-20250308-WA0100.jpg


Daga Katsina Times

Muhammad Yusufu Musawa, hadimin dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Musawa da Matazu, Abdullahi Aliyu Ahmed, ya ajiye aikinsa bisa dalilan da ya bayyana a matsayin na kashin kansa.

A wata takarda da ya aike wa dan majalisar a ranar 4 ga watan Maris, 2025, Muhammad Yusufu ya bayyana godiyarsa bisa damar da aka ba shi, tare da neman afuwa kan duk wata matsala da yin murabus dinsa ka iya haifarwa.

A cewarsa:
"Cikin girmamawa, ina godiya ga damar da ka bani, amma bisa wasu dalilai na kashin kaina da hidimar dake kaina, na yanke shawarar ajiye mukamin da ka bani na ‘Legislative Aid.’ Ina kuma bada hakuri kan duk wata damuwa da hakan zai iya haifarwa."

Binciken Katsina Times ya gano cewa Muhammad Yusufu, wanda kuma ma’aikaci ne a karamar hukumar Musawa, ya koma bakin aikinsa na farko. Sai dai, har yanzu ba a iya gano takamaiman dalilin da ya sa ya ajiye aikin nasa ba.

Sai dai wannan matakin ya jawo cece-kuce da fassara daban-daban a yankunan Musawa da Matazu, kasancewar Muhammad Yusufu na da kyakkyawar shaida a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana. Wasu na ganin irin mutanen da ake bukata a siyasance su ne irin sa, musamman tare da ‘yan siyasar da ke da zababben mukami a Abuja.

A wani bangare, ana tuna cewa dan majalisar, Abdullahi Aliyu Ahmed, shi ne wanda aka nada a matsayin Dujimman Katsina watannin baya. Wannan ne karon farko da ya tsaya takara, kuma ya samu nasarar lashe kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Musawa da Matazu.

Follow Us