Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Nazarin Mallakar Tsohon Garin Gozaki a Karamar Hukumar Kafur

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07032025_130621_FB_IMG_1741352709730.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamitin na wucin gadi domin nazari da bayar da shawarwari kan mallakar tsohon garin Gozaki da ke Karamar Hukumar Kafur, da ake zargin wani kamfani da shi don aiwatar da shirin gina Gozaki Resort.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Garba Faskari, ne ya kaddamar da kwamitin a madadin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, a wani taro da aka gudanar ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025. A ofishin sakataren Gwamnatin dake sakatariyar gwamnatin jihar Katsina 

Kwamitin ya kunshi Membobi Kamar haka

1. Kwamishinan Ma'aikatar Noma (Shugaban Kwamitin)

2. Kwamishinan Ma’aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki (Mamba)

3. Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu (Mamba)

4. Wakilin Majalisar Sarakunan Katsina (Mamba)

5. Wakilin Kungiyoyin Farar Hula (Mamba)

6. Wakili daga Ofishin Gwamna (Sakatare)

Ayyukan da Aka Danka wa Kwamitin sun hada da. Tattaunawa da bangarori masu ruwa da tsaki domin tantance yiwuwar mallakar tsohon Gozaki da kuma ingancin shirin.

Bibiyar girman filin da ake bukata da kuma yiwuwar amfani da karamin yanki idan hakan zai wadatar.

Nazarin yadda za a biya diyya ga masu filaye da la’akari da tarihin yankin, albarkar gonaki da kuma itatuwan kuka da ke yankin.

Kimanta ribar da shirin zai haifar ga gwamnati, kamfanin da zai zuba jari, da al’ummar yankin.

Bayar da shawara kan hanyoyin wayar da kan jama’a domin samun goyon bayan al’umma idan an ga dacewar aiwatar da shirin.

Ba da shawarwari kan matakan tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummar Gozaki da hukumomi.

Kokarin hada kwararru da za su taimaka wa kwamitin a aikinsa.

Mikawa gwamnati rahoto na karshe cikin makonni biyu daga ranar kaddamarwa.

Rahoton da kwamitin zai gabatar zai zama jagora ga gwamnatin Katsina wajen yanke hukunci kan mallakar tsohon Gozaki da kuma aiwatar da shirin Gozaki Resort.

Follow Us