Gwamnatin Katsina Ta Kafa Kwamitin Sake Bude Kasuwannin Shanu Na Batsari da Sheme

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07032025_114205_Screenshot_20250217-233618.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times. Katsina Nijeriya, 6 Ga Maris, 2025 – 

Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa wani kwamitin bincike domin duba yiwuwar bude kasuwannin Batsari da Sheme, sakamakon bukatar jama’a na dawo da kasuwancin su.
Abdullahi Garba Faskari 

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ne ya sanar da kafa kwamitin a madadin Gwamna Malam Dikko Umar Radda a ofishin sa dake sakatariyar jihar Katsina a ranar Alhamis.

Kwamitin ya kunshi manyan jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki, ciki har da: Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Jama’a, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Babbar Lauya/Kwamishiniyar Shari’a ta Jihar Katsina, Mai Baiwa Gwamna Shawara Kan Cigaban Kasuwanni, Shugabannin Kananan Hukumomin Batsari da Faskari, Wakilan hukumomin tsaro kamar su: Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar NSCDC, Jami’an ‘Yan Sanda na Batsari da Faskari, Kwamandan Hukumar Kula da Tsaro ta Al’umma (Community Watch Corps), Shugabannin addini da kungiyoyin kasuwanni ciki har da: Wakilan Darikun Izala da Darika, Shugabannin Kungiyar Kasuwannin Kara, Hakiman Batsari da Faskari, Wakili daga Ofishin Gwamna.

Abdullahi Garba Faskari yace, Kwamitin zai gudanar da ayyuka kamar haka: Tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan batun bude kasuwannin. Tantance matsalolin da ka iya tasowa sakamakon bude kasuwannin. Fitar da matakan da za su magance wadannan matsaloli. Bayar da wasu shawarwari da suka dace. Daukar duk wani mutum da zai taimaka wajen gudanar da aikin tare da Mikawa gwamnati rahoto cikin makonni biyu.

Matakin kafa wannan kwamitin na nuna yadda gwamnatin jihar ke kokarin daidaita batun farfado da tattalin arziki tare da tabbatar da tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Follow Us