Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kurfi Da Dutsamma Ya Raba Mashina Da Kayan Abinci A Kananan Hukumomin.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04032025_101942_IMG-20250304-WA0009.jpg



Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomi Kurfi da Dutsamma Hon. Aminu Balele Dan Arewa, ya kaddamar da rabon Mashina guda talatin ga magaddai na kananan hukumomi Kurfi da Dutsamma domin saukaka masu zirga zirga.

Hakanan kuma ya raba abinci wadanda ya haɗa da shinkafa, da makaroni guda dubu uku ga al'umma domin gudanar da azumin watan Ramadan cikin jin daɗin. 

Taron kaddamar da kayayyakin ya gudana ne a ranar Litinin 03 ga watan Maris 2025, a kofar gidan hakiman guda biyu. Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, da kuma ciyamomi na kananan hukumomin da kuma shugabannin jam'iyya duk sun halarci taron kaddamawar.


A jawabin makasudin bayar da tallafin, Hon Amimu Balele Dan Arewa, ya shaida ma al'umma cewa kasantuwar wahalhalun da magaddai ke sha wajen isar da sakon hakimai zuwa ga al'umma, ya sanya shi tunanin samar masu da wani abu wanda zai dauke masu wadannan wahalhalun da suke yi.

Sannan ya bayyana shirin shi na gaba na sake fasali tare da gyara gidajen hakiman da kuma masallatai, da kuma ci-gaba da kawo abubuwan cigaba wadanda zasu saukaka yanayin da al'ummar da yake wakilta suke ciki.

Shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar Katsina, a jawabin da ya gabatar, ya yi jinjina ga dan Majalisar tarayyar wajen namijin kokari da yake yi domin taimaka ma al'ummar da yake wakilta da kuma samar masu da jin dadi na romon dumukradiya.

Hakiman wadanda suka samu wakilci a wajen taron, sun mika godiyar su ga Allah madaukakin sarki, da kuma gwamnatin jihar Katsina, da kuma ɗan majalisar su, tare da yi mashi fatan alkairi, da kuma addu'ar cigaba da abubuwan alkairi da yake yi a kananan hukumomin.

Follow Us