An haifi Jose Mujika ranar 20 ga watan Mayu na shekara 1935, an haife shi Montevideo babban birnin ƙasar Uruguay. Kuma iyayensa talakawa ne ƙwarai, asalinsu 'yan ci rani ne daga ƙasar Italiya su ka je suka zauna a Uruguay.
Tun ya na ɗan saurayi ya shiga rundunar yan tawayen Tupamaros wadda ta yi gwagwarmaya da dakarun gwamnatin Uruguay.
A cikin wannan fada ne sojoji gwamnati suka caflke shi a matsayin fursuna sai da ya share shekaru 14 a tsare a kurkuku daga 1973 zuwa 1985. Daga cikin shekaru 14 da yayi na zaman gidan kurkuku, yayi shekaru biyu tsare cikin rijiya sai dai a zura masa abinci ya na ciki.
An sako shi daga kurkuku a shekara 1985 bayan da ƙasar Uruguay ta rungumi tsarin mulkin demokraɗiyya.
Bayan an sako shi daga gidan yari 'tare da wasu abokan gwagwarmaya, sai su ka kafa jam'iyar siyasa da suka radawa suna MLN-T, domin ƙwatar mulki ta hanyar demokraɗiyya, wato kenan sun ajiye makamai.
A ƙarƙashin wannan jam'iya ne aka zaɓe shi a matsayin dan Majalisa, ya zama Sanata, kafin daga bisani a naɗa shi ministan noma da raya ƙasa. Ya shiga zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2009, inda ya samu nasara tare da kashi 53 na ƙuri'un da aka kaɗa.
An rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Uruguay a ranar ɗaya ga watan Maris na shekara 2010.
Mai yasa aka cewa shi ne shugaban ƙasar da ya fi ko wane shugaban kasa talauci a duniya?
Na farko tun lokacin da aka rantsar da shi ya ce albashinsa na shugaban ƙasa da yake samu kimanin Euro 10.000 ko wane wata, zai ware kashi 90 cikin dari ga ƙungiyoyin bada agaji ko kuma ga mabuƙata, wato daga cikin wannan kuɗaɗe Euro 10.000 zai ɗauki Euro 1000 kaɗai sun wadace shi, sauran ya bayar ga mabuƙata.
Sannan gidan da yake ciki, irin gidan nan ne na gona. A Turai har ma da ƙasashen Afirka, manoma kan sanya 'yan bukkoki cikin gonarsu, saboda rage yawan kai da komo, daga gida zuwa gona, to marigayi shugaban Mujika a cikin irin wannan gida ya ke, kuma gidan ma ba na shi ne ba, na matarasa ne mai suna Lucia Topolansky. Saɓanin ƙasashen Afirka in da gidan shugaban ƙasa ke jibge sojoji rike da makamai, a gidan shugaban a lokacin 'yan sanda biyu ne rak ke gadi.
Kullum safiya da yake gidan ba cikin gari ya ke ba, sai ya tuko kansa cikin tsohuwar motarsa kirar Bitil zuwa wurin aiki da yamma kuma ya tuka ya koma gida ba tare da jiniya ba ko wata tawagar soja.
Idan ma dai ba kan san motarsa ba, idan da ya wuce ba za ka iya gane shugaban ƙasa ne ba. Sannan abun mamaki har mutu bai bar noma ba, aikin da ya saba yi shi da matarsa kamin a zaɓe shi shugaban ƙasa shi ya cigaba da yi bayan ya sauka.
Kafofin sadarwa da dama sun yi ta zuwa gidansa suna hira da shi, suna tambayarsa mai yasa ya ke rayuwa haka cikin talauci, alhali ga shi ya samu matsayin shugaban ƙasa?. Amsar da yake ba su kullum iri guda ce: Ya na ce masu ni ba matalauci ba ne, ba na bukatar facaka ne a rayuwata, ya na basu misali da babban ma'aikaci a Uruguay albashin sa Euro 900 a wata, kuma ya isheshi yin rayuwa, saboda haka bai ga dalilin da zai sa shi ya ɗau albashi fiye da haka ba.
Ya na ce musu shi a tunaninsa rayuwa abu uku ne zuwa huɗu wato soyyaya, mutum ya so dan uwansa, sannan iyali, da kuma aminai.
Shi kuɗi a gare shi ba abun damuwa ne ba, saboda idan ya tara su nan duniya zai bar su, saboda haka a maimakon ya yi ta tara kudi ya fi dacewa ya ɗauki abinda zai ishe shi sannan sauran ya taimakawa mabuƙata.
Sannan ya na ce masu a tsawan rayuwarasa ya share shekaru 14 kulle a kurkuku, daga cikin shekarun biyu yayi su a cikin rijiya, kuma kamin ma a kama shi yayi fiye da shekaru goma bai da katifa, sai dai ya shimfiɗa tabarma a ƙasa ya kwanta. Saboda haka kimamin Euro dubu da ya ke samu ko wane wata sun ishe shi yayi rayuwarsa cikin rufin asiri.
To kun ji kaɗan daga dalilan da suka sa ake cewa shugaban kasar Uruguay marigayi Jose Mujika shi ne ya fi kowane shugaban kasa talauci a duniya.
Kuma duk da haka ba shi da wata matsala, yadda ka san ko wane shugaba ya na gudanar da mulki shi ma haka. Kuma a lokacinsa, al'umar Uruguay sun ga canji sosai ta fannin cigaban ƙasa saboda an samu raguwa ta fannin cin hanci da rashawa, saboda kyakkyawan misalin da shugaban ke badawa.
Sannan a lokacin mulkin sa tauraruwar Uruguay ta na haskakawa kwarai a yankin kasashen Latin Amurka, da kuma a Majalisar Dinkin Duniya, domin ƙasar ta na bada gudummuwa sosai a aiyukan Majalisar.
A zamanin mulkinsa Mujika, Uruguay ce ƙasa ta biyu a yankin Lati Amurka bayan Brazil ta fannin bada tallafi mai yawa ga Majalisar Dinkin Duniya.
A taƙaice dai kafofin sadarwa sun nunar da cewa lalle duk ɗan Adam ajizi ne, ba zai rasa kura-kurai ba, amma haƙiƙa ɗabi' o' in tsohon shugaban Uruguay abin koyi ga shuganin ba ma na Afrika har ma na sauran ƙasashen duniya.
Mutuwa
Mujica ya mutu a washegarin 13 ga Mayu 2025, mako guda kafin cikarsa shekaru 90, a gidan gonarsa da ke Rincón del Cerro, a wajen Montevideo; Orsi ne ya sanar da rasuwarsa. Gwamnatin Uruguay ta bayyana kwanaki uku na zaman makoki na kasa.