Ziyarar Hukumar Ilimin Manya: Sarkin Dawan Katsina Ya Karɓi Tawagar NMEC da Hukumar Ilimin ta Jihar Katsina a madadin Sarki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27022025_231248_FB_IMG_1740697580730.jpg


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 27, Fabrairu 2025

A ci gaba da kokarin farfaɗo da ilimin manya a jihar Katsina, wata tawaga daga Hukumar Ilimin Manya ta Ƙasa (NMEC) tare da Hukumar Ilimin Jihar Katsina sun kai ziyara Masarautar Katsina a ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, 2025. Sarkin Dawan Katsina, Alhaji Abba Balarabe, ya tarbi tawagar a madadin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman, CFR.

Ziyarar na cikin shirin gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda, PhD, na farfaɗo da makarantun manya tare da tabbatar da shigar da dukkanin gundumomin hakimai da dagatai a cikin shirin.

A cikin jawabinsa, Sarkin Katsina ya jaddada muhimmancin ilimi ga ci gaban al’umma tare da nuna goyon bayansa ga shirin maido da tsarin da aka watsar da shi a baya. Ya bukaci dukkanin hakimai da su karɓi shirin tare da tabbatar da ingantaccen aiwatarwa a yankunansu.

Shugaban tawagar, Alhaji Yusuf Abdulkadir Aliyu, Koodinetan shiyyar Arewa maso Yamma na NMEC, ya bayyana cewa hukumar na da aikin tsara manufofin ilimin manya da tabbatar da aiwatar da su a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

"Ayyukanmu shi ne ƙirƙirar manufofin ilimin manya da miƙa su ga jihohi domin su aiwatar, wanda hakan ke bada damar isar da ilimi zuwa mafi nisa na yankunan karkara," in ji shi.

A nata bangaren, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai, Babbar Daraktar Hukumar Ilimin Jiha ta Katsina, ta jaddada cewa gwamnatin jihar na da kudirin yaƙi da jahilci da rashin aikin yi, domin waɗannan abubuwa ne ke haifar da matsalolin tsaro.

"Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya himmantu matuƙa wajen yaƙi da jahilci da rashin aikin yi. Ba kawai ilimin boko muke mayar da hankali ba, har da ilimin addini da koyar da sana’o’i domin mutane su samu damar dogaro da kansu," in ji ta.

Hajiya Kaikai ta roki goyon baya da shawarwari ga Masarautar Katsina tare ba da ƙarin goyon baya wajen samar da cibiyoyin ilimi a gidajen sarakuna da hakimai na masarautar Katsina.

Haka zalika Tawagar tana bincike tare da duba duk wasu cibiyoyi na Ilimi da suke aiki ba ya amma yanzu aka watsar da su don nazarin sake gyara su da farfado dasu daidai da zamani.

Ziyarar wannan tawaga zuwa Masarautar Katsina na nuna irin matakan da ake ɗauka don farfaɗo da ilimin manya a jihar. Tare da haɗin gwiwar masarautu, gwamnati, da al’umma, ana fatan cimma burin ƙarfafa ilimi da sana’o’i, wanda zai taimaka wajen rage jahilci da rashin aikin yi a jihar Katsina.

Follow Us