An ja hankalina zuwa ga wata hira da akai da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a yammacin ranar Litinin.
Ba dan za a iya fassara shiru na da cewa na yarda da abubuwan da ya furta ba, da na yi watsi da shi da kalaman sa. A halin yanzu na shagaltu da tarin ayyukan da suke gaba na, ba zan tsaya cece-kuce da Nasir El-Rufai ba ko wani a kafafen yaɗa labarai ba.
Duk da cin zarafi da hare-haren da yake yi a kaina, babu inda na taba magana mara kyau akan Nasir. Na kame ne saboda mutunta tsohuwar alaƙar mu ta baya da kuma ta danginmu. Kuma ba zan fara yau ba.
Duk da haka, ina kira ga jama'a da su yi watsi da maganganun El-rufai akai na.
Don kaucewa shakku, ina tabbatar muku da cewa ban taba tattauna batun takarar shugabancin ƙasar nan a 2031 da kowa ba. Dukkan tunani na da ƙoƙari na a yanzu sun karkata ne ga ci gaban Najeriya da nasarar gwamnatin shugaba Tinubu.
Don haka ina rokon Nasir El-Rufai da ya ƙyale ni in fuskanci babban aikin dake gabana na kasa kamar yadda ban damu kaina da shiga lamuransa ba.
Nuhu Ribadu