An fara Horan Sulhu na Kwana Hudu ga Shugabannin Gargajiya A Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24022025_184242_FB_IMG_1740421052061.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 


An fara horon sulhu na kwanaki huɗu ga shugabannin gargajiya a Katsina, wanda ake gudanarwa a Otal ɗin Hujrat daga ranar 24 zuwa 28 ga Fabrairu, 2025. Horon na da nufin ƙarfafa rawar da shugabannin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da warware rikice-rikice a yankunansu.

Taron ya tattaro manyan shugabannin gargajiya, ciki har da Sarkin Fulani Dangi, Alhaji Lawal Bagiwa, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman, da sauran shugabanni daga yankunan Katsina da Charanchi.

A jawabin sa, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya ga ci gaban al'umma.

"Ba za a samu ci gaba ba tare da zaman lafiya ba. Duk wani shiri da ke da nufin inganta zaman lafiya yana da matuƙar muhimmanci. Tun da dadewa, shugabannin gargajiya suna taka muhimmiyar rawa a wannan fanni, don haka yana da kyau a ƙara masu ilimi kan sabbin hanyoyin sasanta rikice-rikice," in ji shi.

Ya gode wa shirin Spring Programme, wanda Gwamnatin Birtaniya ke daukar nauyinsa, tare da yabawa cibiyar Green Horizon da ke gudanar da horon. Haka nan, ya gode wa Mai Martaba Sarkin Katsina, Dr. Abdulmumini Kabir Usman, bisa goyon bayan sa ga wannan shiri.

Shugaban tawagar shirin Spring Programme, Dr. Okoha Ukiwo, ya bayyana cewa shirin yana da burin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya. Ya ce Gwamnatin Birtaniya na da damuwa kan halin da kasar ke ciki, domin rashin zaman lafiya a Najeriya na iya shafar dukan Afirka.

"Mun yi nazari kan matsalolin tsaro da zaman lafiya a Arewacin Najeriya, kuma muna aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita. Mun fahimci cewa shugabannin gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikice-rikice, don haka muna kokarin ƙarfafa basirarsu domin tabbatar da zaman lafiya," in ji shi.

Farfesa Muhammad Tabiu (SAN) daga Green Horizon, wanda ke jagorantar horon, ya bayyana cewa shugabannin gargajiya suna da nauyin tabbatar da daidaito a al’umma. Ya ce horon zai basu ƙarin ilimi kan sulhu da rigakafin rikici, tare da koyar da su yadda za su iya aiki tare da hukumomin tsaro da shari’a cikin lumana.

"Babban burin horon shi ne ƙara wa shugabannin gargajiya kwarewa wajen sasanta rikice-rikice. Idan al’umma suka yarda da shawarwarin da suke bayarwa, hakan zai taimaka wajen dakile tashin hankali," in ji shi.

Shirin zai kuma mayar da hankali kan hana yaduwar makamai, rage amfani da miyagun ƙwayoyi, da inganta dangantaka tsakanin manoma da makiyaya.

Ana sa ran wannan horo zai zama matakin farko na faɗaɗa irin wannan shiri zuwa wasu yankunan Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Follow Us