Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 82, tare da kama 198, tare da ceto mutane 93 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda.
Daraktan Hulɗa da Manema Labarai na Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da sabbin bayanai kan ayyukan rundunar a ranar Juma’a a Abuja.
A cewarsa, sojojin sun kuma kwato makamai 152 da alburusai iri-iri tare da wasu kayayyakin yaki da suka hada da. Bindigogi 86, AK-47 guda 46, da kanana 18 da wasu 19 na gargajiya. Alburusai 2,040 na nau’uka daban-daban, ciki har da 1,165 na 7.62mm Special da 128 na 7.62mm NATO.
Haka nan, dakarun sojojin sun cafke mutane 22 da ke da hannu a satar man fetur a yankin Kudu maso Kudu, tare da dakile asarar mai da kudinsa ya kai Naira miliyan 587.
Bugu da kari, ‘yan ta’adda 41 sun mika wuya a yankin Arewa maso Gabas, tare da makamai da alburusai da suka hada da PKT gun, AK-47 da bindigar AK-101.
Kangye ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a duk fadin Najeriya