Gwamna Radda Ya Kaddamar da Raba Akuya 40,000 Don Bunkasa Kiwo a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17022025_160244_Screenshot_20250217-164733.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da shirin raba akuya 40,000 ga manoma domin bunkasa kiwo da habaka tattalin arziki. Shirin, wanda aka ware wa naira biliyan 5.7, na da nufin mayar da Katsina cibiyar kiwo a Najeriya tare da inganta rayuwar mata ta hanyar samar da dabbobi masu yawa.

A yayin kaddamar da shirin a karamar hukumar Daura, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan mataki wata alama ce ta sabuwar hanyar da gwamnatin sa ke bi don habaka kiwo.

Manufar Shirin

Shirin yana da nufin tallafa wa mata ta hannun ma’aikatar harkokin mata da kwamitocin al’umma. Kowace mazaba za ta amfana da mata 10 da kuma babban manomi guda, inda kowacce mata za ta samu akuya hudu—namiji daya da mata uku—yayinda babbar gonar kiwo za ta karɓi akuya 50.

Bugu da ƙari, za a bai wa manoma horo kan dabarun kiwo na zamani, ilimin ciyar da dabbobi, kula da lafiyarsu, da dabarun noma na zamani.

Tallafi da Hanyoyin Biya

Gwamnatin jihar ta samar da tsarin rance mai sauki don bai wa manoman damar biya cikin sauki bayan wani lokaci. Haka nan, an samar da cibiyoyi uku na kula da kiwo domin tabbatar da lafiyar dabbobin kafin rabawa.

Gudunmawar Gwamnati da Manyan Jiga-Jigai

Gwamna Radda ya gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa kafa ma’aikatar raya kiwo a Najeriya, tare da tabbatar da cewa Katsina za ta ci gaba da tallafa wa manoma. Haka kuma, an shirya kafa gonar kiwo a karamar hukumar Rimi don habaka nau'in akuyoyin da inganta samar da madara da takin zamani.

Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua, ta yaba da shirin, tana mai cewa zai taimaka matuka wajen habaka rayuwar mata.

Shi ma, Mai Bai Wa Gwamna Shawara Kan Kiwo da Filayen Kiwo, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya jaddada cewa shirin zai kara karfin mata wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma.

Sarakuna da Masu Ruwa da Tsaki Sun Yaba

Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruk Umar Faruk, ya jinjinawa Gwamna Radda bisa kokarin da yake yi na habaka tattalin arzikin jihar.

Shirin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, mambobin majalisar zartarwar jiha da sauran masu ruwa da tsaki.

Follow Us