Katsina Times
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya nuna damuwa kan yadda wasu malamai ke kara tsunduma cikin harkokin siyasa, yana mai cewa yanzu suna da babban tasiri a kan masu kada kuri’a da tsarin zabe gaba daya.
Lamido ya yi wannan furuci a wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna sakamakon rasuwar babban dansa.
Tsohon Ministan Harkokin Waje ya koka da cewa malamai sun mamaye fagen siyasa, inda suke fitowa fili suna goyon bayan ‘yan takara tare da umartar mabiyansu su zabi wanda suka yarda da shi.
“Duk da albarkar da Allah ya ba su na shugabancin addini, yanzu malamai suna fafutukar neman mulki. Malamai ya kamata su zama masu shiryar da ‘yan siyasa, amma tunda suna son mulki, mu ‘yan siyasa mun ja da baya muna kallo. Muna jiran su fada mana wanda za mu zaba bisa ga bukatarsu. A gaskiya, kowa ya kamata ya tsaya a matsayinsa domin adalci da daidaito a al’umma,” in ji shi.
Lamido ya kara da cewa kamar yadda jam’iyyun siyasa ke fama da rikice-rikicen cikin gida, haka ma kungiyoyin addini ke da rabuwar kai, yana gargadin cewa siyasar Najeriya ba za ta tsira daga rudani ba matukar ba a samu hadin kai ba.
A baya, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa manyan malamai sun taka muhimmiyar rawa wajen kwadaitar da mabiyansu su yi rajistar zabe. Sai dai a zaben 2023, wanda aka fi ganin a matsayin daya daga cikin mafi rikitarwa a tarihin Najeriya, majami’u da masallatai sun wuce matsayinsu na jan hankalin jama’a kan muhimmancin kada kuri’a, inda suka rika fitowa fili suna mara wa ‘yan takara baya.
A lokacin hudubobi da wa’azozi da aka gabatar a masallatai da majami’u, an yi amfani da su wajen tallata wasu ‘yan takara. A wasu coci-coci, an yi ikirarin cewa wasu daga cikin ‘yan takara suna da “mandatar Ubangiji,” yayin da a masallatai, wasu malamai suka bukaci mabiyansu su zabi ‘yan takara bisa la’akari da addini. Abin sha’awa, da dama daga cikin wadannan annabce-annabcen ba su tabbata ba.
A kwanan nan, wata takaddama ta kunno kai game da shirin wani babban taron Al-Qur’ani da aka tsara yi a ranar 22 ga Fabrairu 2025 a Abuja, inda ake sa ran mutane 30,000 da suka hada da masu haddar Qur’ani, marubuta, makaranta, da masu zane-zane za su halarta. Sai dai an dage taron nan take bayan wasu malaman addini sun yi shakku game da amincinsa, suna zargin cewa wata dabara ce ta siyasa da ke da alaka da zaben 2027.
Idan aka tuna, tikitin Muslim-Muslim na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 ya kusa haddasa rabuwar kawuna a siyasar kasar, amma ya tsira ne saboda goyon bayan da ya samu daga wasu manyan malamai da suka tabbatar wa mabiyansu cewa tikitin yana da albarka. Baya ga haka, son zuciya na kabilanci da na yankin kudu maso yamma ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar sa.
A lokacin zaben 2023, magoya bayan Tinubu a arewacin Najeriya sun yi kokarin jawo manyan malamai don samun goyon bayansu. Yanzu ana ganin irin wannan dabarar tana sake dawowa yayin da ‘yan siyasa ke fara shirin 2027.
A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, ana ganin yana kokarin sake tsara kamanninsa a yankin arewa mai rinjayen Musulmi gabanin zaben gaba. Halartar sa wajen cin abincin bude baki a lokacin azumi da kuma taimakawa al’umma da kudade ana ganin wata hanya ce ta samun goyon bayan manyan malamai.
Magoya bayan Obi na ganin cewa, banda zargin magudin zabe, rashin neman goyon bayan manyan malamai na arewa ne ya hana shi nasara a 2023. Yanzu, yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, ‘yan tawagarsa na kokarin gujewa sake maimaita wannan kuskuren.