Sarautar Magajin Garin Katsina wata babbar sarauta ce da ke da kusanci da gidan sarauta. Ana ba da wannan mukami ne ga babban ɗan sarki ko wanda sarki ya zaba daga cikin ‘ya’yansa. Wannan sarauta tana da kama da ta Chiroma a Kano, wanda ke da dama mai yawa ta zama sarki a nan gaba. Duk da haka, sarautar sarki tana bisa ga nufin Allah, wanda ke bayar da mulki ga wanda ya so.
A shekara ta 1906, Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya zama sarki na farko a gidan Fulani Sullubawa. Kafin haka, a ƙarshen shekarun 1890s, lokacin da ‘yan bassa suka addabi yankin Kano, Sarkin Katsina Abubakar ya tura Muhammadu Dikko—wanda a lokacin ke da sarautar Danbarhim—zuwa Kusada don hana bassa kutsawa Katsina, yayin da sarki Abubakar ya zauna a Kankiya yana jiran lokaci mai dacewa.
Lokacin da Durbi Sada, ƙanen mahaifin Muhammadu Dikko, ya rasu, Sarkin Katsina Abubakar ya aika wa Muhammadu Dikko ya zo Kankiya. Bayan isarsa, sai ya sauka a gidan wani attajirin Fulani mai suna Gyarta Gari. Da safe, bayan ya gaishe da sarki, sai Sarkin Katsina Abubakar ya ba shi Sarautar Durbi, ya cire hular kansa ya dora masa, inda aka nada shi Durbin Katsina.
Mutumin da Muhammadu Dikko ya sauka a gidansa—Gyarta Gari—yana da ɗa mai suna Dogo (Abubakar). Bayan Muhammadu Dikko ya gode masa, sai ya ba shi dansa Dogo amanar reno. Wannan Dogo ne ya zama Magajin Garin Katsina na farko a zamanin Fulani Sullubawa.
Magaji Gari Dogo (Abubakar) (1907-1913)
Magaji Gari Muhammadu Zayyana (1913-1928)
Magaji Gari Usman Nagogo (1928-1944)
Magaji Gari Yusuf Lamba (1944-1949)
Magaji Gari Abubakar Duwan (1949-1960)
Magaji Gari Muhammadu Kabiru Usman (1960-1981)
Magaji Gari Abdulmuminu Kabir Usman (1982-2008)
Magaji Gari Ahmadu Tijjani Kabir Usman (2008-2009)
Magaji Gari Aminu Abdulmuminu Kabir Usman (2013 – Yanzu)
Tun daga fara mulkin Fulani Sullubawa, an samu tara (9) daga cikin Magajin Gari a Masarautar Katsina. Cikin su, bakwai (7) sun fito daga gidan sarki, yayin da uku (3) suka zama sarakunan Katsina.
Wannan jerin suna na Magajin Gari yana da muhimmanci a tarihin Katsina, kasancewar mukamin yana da matsayi mai girma a masarauta. Sarautar Magajin Gari tana nuna kusancin mai rike da shi da gadon sarauta, sai dai ba lallai ne ya zama sarki ba, domin komai yana tafiya ne bisa ga kaddarar Ubangiji.
Fans
Fans
Fans
Fans