SULHU DA ’YAN BINDIGA BA ZAI TAƁA ZAMA DAGA CIKIN TSARIN MU BA – GWAMNAN ZAMFARA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11022025_225825_IMG-20250211-WA0046.jpg


Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba ta da niyyar yin sulhu da ’yan bindiga a jihar.

An yi wa gwamnan gurguwar fassara a wata hira ta musamman da ya yi da Sashen Hausa na BBC a ƙarshen mako.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce wasu kafafen yaɗa labarai sun fassara hirar da gwamnan yi da sashen Hausa na BBC a hagunce domin a yaudari jama’a kan matsayin gwamnatin jihar.

Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta samu nasarar yaƙi da ‘yan ta’adda ta hanyar amfani da tsauraran dabaru na kai farmaki kan ’yan bindigar da ke jihar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Batun ‘yan bindiga ya kasance abin damuwa ga al’umma a faɗin Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma ƙasar baki ɗaya tsawon shekaru da dama.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin.

“A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin.

“Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, kuma ta ɗauki matakin da ya dace tun farko cewa sulhu da ‘yan bindiga ba komai ba ne illa ‘je ka na yi ka’.

“A cikin hirarraki da manema labarai daban-daban, gwamnan ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yo sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba.

“Ya kamata a bayyana a sarari kuma a rubuce cewa matsayin Gwamna Dauda Lawal ya kasance babu cece-kuce: babu wata gwamnati da ta san ciwon kanta da za ta yi sulhu da masu kisa.

“Tattaunawar da Gwamna Lawal ya yi da BBC Hausa ya nuna cewa matsayinsa ƙarara yake ba tare da boye-boye ba. Ya ci gaba da cewa, tun da farko idan aka samu damar sulhu, to dole ne ‘yan bindigar su miƙa wuya su tuba tare da ajiye makamansu ba tare da wani sharaɗi ko buƙata ba.

“Dabarun da muke aiwatarwa na yaƙar ‘yan bindiga na samar da sakamako mai kyau, saboda yawancin yankunan jihar da ke fama da rikici na samun dawowar zaman lafiya. Abin da ake ƙara samu a Zamfara shi ne irin nasarorin kawar da shugabannin da ɗaruruwan ’yan bindiga a kullum.”

Follow Us