'Yan Fashi da Makami Sun Tare Hanyar Charanchi da Kankia

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10022025_163515_KatsinaTimes02012024_183110_FB_IMG_1704220069464.jpg


Gamayyar Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Su

Daga Katsina Times

A ranar Asabar, 8 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 6:00 na safe, wasu 'yan fashi da makami sun tare hanyar da ke tsakanin Charanchi da Kankia, a kusa da kauyen Dan Na Yaki, domin yin fashi ga motocin da ke kan hanyar zuwa Kano don harkokin kasuwanci.

‘Yan fashin sun kafa shinge da nufin aiwatar da mugun aikinsu, sai dai ba a jima ba sai ga tawagar shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina, Alhaji Lawal Faskari. A cikin tawagar akwai gamayyar jami’an tsaron hukumar, da ma’aikatan DSS, tare da ‘yan sanda.

Jami’an tsaron ne suka dakile harin ta hanyar bude wuta, lamarin da ya sa ‘yan fashin suka tsere cikin daji.

Jaridar Taskar Labarai ta samu tabbacin faruwar lamarin daga wadanda abin ya shafa da kuma jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina.

Direbobin da ke bin hanyar zuwa Kano sun tabbatar wa da jaridar Katsina Times cewa ‘yan fashi da makami sun daɗe suna tare hanya, suna kwace kuɗaɗen fasinjoji, musamman a ranakun kasuwanni da lokutan da jama’a ke tafiya Kano.

Follow Us