Mataimakin Gwamnan Katsina Ya Yi Kira Ga Dalibai Su Taka Rawa Wajen Ci Gaban Al’umma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09022025_002044_FB_IMG_1739060346310.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times – 8 ga Fabrairu, 2025

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal Jobe, ya bukaci daliban da suka kammala karatu a Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a ta Yusuf Bala Usman da ke Daura, su yi amfani da iliminsu wajen ci gaban al’umma. Ya bayyana hakan ne yayin da ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda Ph.D, a bikin yaye dalibai karon farko da kwalejin ta shirya a ranar Asabar, 8 ga Fabrairu, 2025.  

A jawabin nasa, Malam Jobe ya jaddada muhimmancin ilimi a matsayin ginshikin ci gaba, inda ya bukaci daliban da su yi amfani da damammakin da suka samu domin bunkasa kansu da kuma taimakawa wajen habaka jihar. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da kokari wajen kyautata harkokin ilimi da samar da ingantaccen yanayi na samun nasarar ilimi da sana’o’i.  

“Muna da aniyar karfafa dalibai domin su fuskanci makoma mai cike da sanin ya kamata da kishin rayuwarsu, ba wai kawai su dogara da neman dama a ketare ba. Ina kira ga dukkan dalibai da su yi amfani da wannan dama da kyau,” in ji shi.  

Haka kuma, Mataimakin Gwamnan ya nuna godiyarsa ga shugabanci da malamai na kwalejin bisa kokarin da suke yi wajen tabbatar da ingancin ilimi. Ya bukaci daliban da su kasance masu rikon gaskiya, hakuri da jajircewa a rayuwarsu ta gaba.  

Bikin dai ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar, inda aka mika takardun shaidar kammala karatu ga dalibai na farko da suka kammala a wannan babbar cibiyar ilimi, tare da mika kyaututtukan Karramawa ga wasu fitattun jihar Katsina, irin su tsohon shugaban Nijeriya marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua, da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Dattijo Muhammad Sani Zangon Daura CON, Marigayi Dr Yusuf Bala Usman, da Alhaji Lawal Sade Daura.

Follow Us