Justice Mahuta Ya Nisanta Kansa Daga Kiran Yin Watsi da Tinubu, Ya Ce Ba Matsayar Dattawan Katsina Ba Ce

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08022025_192329_FB_IMG_1739042274123.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times, 8 Ga Fabrairu, 2025


Tsohon alkalin alkalan jihar Katsina kuma Galadiman Katsina, Justice Sadiq Abdullahi Mahuta, ya nisanta kansa da kuma Majalisar Dattawan Katsina daga wata magana da ake danganta musu da ke cewa an bukaci al’ummar jihar su yi watsi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.  

Da yake jawabi ga manema labarai a gidansa, Justice Mahuta ya bayyana cewa, kodayake majalisar dattawan ta nuna damuwa kan tsare Farfesa Usman Yusuf ba su taba bayar da wata sanarwa da ke da alaka da siyasa ko zabe ba.  

“Babban abin da ya haddasa taron manema labarai shi ne tsare Farfesa Usman Yusuf. Mun ji wajibi ne a matsayinmu na dattawa mu bukaci a yi masa adalci, ko dai a gurfanar da shi a kotu ko kuma a sake shi. Yanzu dai na samu labarin cewa an sake shi,” in ji Mahuta.  

Sai dai ya jaddada cewa babu wata matsaya daga dattawan Katsina da ta bukaci jama’a su yi watsi da Tinubu a 2027.  

"Wannan ba irin kalaman dattawa ba ne. Ba matsayar mu ba ce. Mun nisanta kanmu gaba daya daga wannan magana," in ji shi.  

Justice Mahuta ya kara da cewa ya tuntubi wasu manyan dattawa a jihar, sanannu, inda wasu suka goyi bayan matsayarsa yayin da wasu suka ki bayyana ra’ayinsu.  

Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Dattawan Katsina a karkashin jagorancin Alhaji Aliyu Sani Muhammad, suka shirya wani taron manema labarai, tare da kira ga shugaba Bola Tinubu da ya saki Farfesa Yusuf ko kuma su kada shi zabe a shekarar 2027.

Follow Us