Tunawa da Gudunmawar Dr. Bala Usman An Karrama Shi, a Bikin Yaye Dalibai na Farko a Kwalejin Yusufu Bala Usman

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08022025_173656_FB_IMG_1739036062025.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 
Hajiya Zainab Bala Usman 

An karrama marigayi Dr. Bala Usman bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ilimi, adalci, da ci gaban al’umma a yayin bikin yaye dalibai na farko na Kwalejin Ilimi da Nazarin Shari’a ta Yusufu Bala Usman, Daura. An gudanar da bikin ne a harabar makarantar da ke kan titin Kano, Daura.  

A madadin iyalan Dakta Bala Usman, Hajiya Zainab Bala Usman ta bayyana matukar godiya bisa wannan karramawa, inda ta jaddada cewa mahaifinsu ya sadaukar da rayuwarsa wajen riko da gaskiya, neman ilimi, da taimakon al’umma fiye da tara dukiya.  

"Mahaifina mutum ne mai gaskiya da jajircewa, wanda bai taba fifita bukatun duniya ba. Ya dauki ilimi da adalci da muhimmanci, kuma yana tafiya tare da kowa da kowa cikin adalci da tausayi," in ji ta.  

Marigayi Dr. Bala Usman ya shahara wajen neman ilimi da kare hakkokin talakawa, kuma gudunmawarsa har yanzu tana da tasiri a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.  

"Wannan karramawa shaida ce ta irin rawar da mahaifina ya taka a fagen ilimi da ci gaban al’umma. Har yanzu sunansa yana ci gaba da haskaka rayuwar malamai da masu fafutukar gaskiya," ta kara da cewa.  

Hajiya Zainab ta kuma gode wa shugabannin kwalejin bisa wannan yabo Karramawa da suka yi wa mahaifinta, tana mai tabbatar da cewa darussan da ya bari za su ci gaba da zama haske ga matasa da malamai masu kishin kasa.  

Marigayi Dr. Bala Usman ya rasu yana da shekaru 66, kuma a watan Satumba zai cika shekaru 20 da barinsa duniya. Duk da haka, sunansa da gudunmawarsa suna ci gaba da rayuwa a zukatan masu ilimi da masu fafutukar adalci.  

Daga cikin sauran manyan mutane da aka karrama a bikin sun hada da tsoffin shugabannin Najeriya, Muhammadu Buhari da Malam Umaru Musa Yar’adua, da kuma fitattun mutane kamar Alhaji Sani Zangon Daura (CON) da Alhaji Lawal Sade Daura, Manajan Darakta na Kamfanin NNPC Trading Company.

Follow Us