Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsaro da tattalin arzikin ƙasar sun inganta sosai a lokacin mulkinsa na tsawon shekaru takwas.
Buhari ya baiyana hakan a jiya Laraba yayin da ya ke karɓar baƙuncin membobin Kungiyar 'Yan Jarida ta Katsina State Correspondents’ Chapel a gidansa da ke Daura, Jihar Katsina.
Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce ya karɓi tattalin arziki mai rauni da ƙalubalen tsaro daga hannun jam’iyyar PDP, wacce ta yi mulki na tsawon shekaru 16.
Amma Buhari ya tabbatar da cewa dabarun gwamnatinsa sun yi nasarar shawo kan waɗannan ƙalubalen, inda aka dakile ta’addanci da matsalolin tattalin arziki.
Ya ce, “Tsaro da tattalin arzikin Najeriya sun inganta sosai a ƙarƙashin mulkina idan aka kwatanta da halin da muka tarar a 2015. Abubuwa za su ci gaba da inganta a Najeriya.”
Haka nan, tsohon shugaban ƙasar ya amince da cewa ƙasar na fama da ƙalubalen shugabanci, yana mai cewa kawai masu riƙe da madafun iko ne ke fahimtar waɗannan matsaloli sosai.
A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar 'Yan Jarida ta Katsina, Yusuf Ibrahim-Jargaba, ya yaba wa kokarin Buhari wajen yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane, da sauran matsalolin tsaro a lokacin mulkinsa.