Daga Abbas Nasir P.R.O (STOWASSA)
Shugaban hukumar Samar da Ruwan sha a matsakaitan birane da tsaftar muhalli ta Jahar Katsina (STOWASSA) Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba yayi yabon a lokacin bikin bayar da tuta ga yan'takarar kansiloli na karamar hukumar.
Kamar yadda Alh Ibrahim Lawal Dankaba ya ce karamar hukumar bata taba samun yawan masu rike da mukamai acikin gwamnati ba kamar ta gwamna malam Dikko Radda, dan haka ya zama wajibi al'ummar kaita su fito kwan su da kwalkwata don tabbatar da samun nasarar jam'iyyar Apc.
Dankaba yace Mu yanzu al'ummar karamar hukumar kaita malam Dikko Radda shike binmu bashi duba da irin karamawar da yayi mana ta baiwa mutanen mu mukamai daban daban wanda ada sai dai mugani ga wasu kananan hukumomi.
Alh Ibrahim Dankaba yasha alwashi tabbatar da bayar da cikakken goyan bayansu ga zaben kananan hukumomi dake tafe domin samun nasarar jam'iyyar APC.
Alhaji Ibrahim Dankaba ya bukaci yan'takarar kansiloli dasu mayar da hankali wajen tallafama al'ummar kamar yanda gwamna malam Dikko Radda ya shawarci duk kan ya'yan jam'iyyar don tabbatar da dorewar nasarar jam'iyyar APC.
A jawabansu daban daban shuwagabanin mazabu 6 da suka sauya sheka daga jam'iyya PDP zuwa APC da suka fito daga Dankaba Ward, Matsai ward, Abdallawa ward, Yanhoho ward, Girka ward da kuma Dankama sun bayyana cewa sun dawo jam'iyyar ne duba da irin salon mulki na gwamna Radda musamman kokarin da yake yi kan yaki da matsalar tsaro da bunkasa bangaren ilimi da kiwon lafiya da sauran bangarori na rayuwar al'umma.
Sauran wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC sun hada da Hon Rabe Manman kaita Alh Manman Dago Dago ,Alh Salisu likita, Hon Murtala Yanhoho da sauran dubban magoya bayan jamiyyun Adawa daba-daban.