Wasu barayin daji sun ba da wa’adin kudi ga mazauna unguwar G.R.A dake garin Dutsinma, jihar Katsina, inda suka nemi a tura musu Naira miliyan goma sha biyar ko kuma su kawo hari a unguwar. Wannan barazana ta janyo tsoro sosai a cikin al’umma, wanda ya sanya mazauna unguwar ke ta yin hijira daga gidajensu, wasu suna tashi zuwa babban birnin Katsina, wasu kuma sun nufi wasu wurare daban-daban.
A yau Litinin, 3 ga watan Janairu 2025, wakilan Katsina Times da suka ziyarci unguwar, sun tarar da mafi yawan gidajen unguwar sun bar wurin. Wasu na daukar kaya kafin dare ya yi. Mazauna unguwar sun tabbatar da cewa Litinin shine ranar da barayin daji suka ba wa mazauna unguwar wa’adin cika kudin fansa ko kuma su kawo hari.
Wannan barazana ta sanya mazauna unguwar cikin damuwa, yayin da wasu daga cikinsu sun bayyana cewa ko kadan ba a samu hada kudin ba, wanda ya sanya kowa ke rayuwa cikin fargaba, saboda babu wanda ya san abin da zai faru a daren yau ko nan gaba.
Mazauna unguwar sun bayyana wa Katsina Times cewa, ko da aka kawo jami’an tsaro, amma galibi, a cikin dare ba sa samun su a lokacin da ake bukatar su. Sun kara da cewa sun hada kai suna gadin unguwar, amma barayin daji suna zuwa da muggan makamai wadanda ba za su iya tunkarar su ba.
Katsina Times ta tuntubi jami’an 'Yan Sandan Jihar Katsina, amma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, ba su samu amsa daga wurinsu ba.
Binciken Katsina Times ya tabbatar da cewa barayin daji sun dade suna kai hare-hare a unguwar G.R.A Dutsinma, suna kuma daukar mutane har sai an biya kudin fansa domin su sako su. Wani daga cikin wadanda aka sako kwanan nan shi ne suka bawa sakon, yana kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin gidajen mazauna unguwar na cikin hatsari.