Manjo Janar Muhammad Dahiru Danja Ya Sabunta Makarantar Firamare a Garin Danja

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02022025_090207_IMG-20250202-WA0016.jpg

Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times 

A ranar Asabar, 1 ga watan Fabrairu, 2025, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya jagoranci bikin kaddamar da sabuwar makarantar firamare a garin Danja, bayan gyaran da Manjo Janar Muhammad Dahiru Danja ya dauki nauyin aiwatarwa.  

Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan jami’an tsaro, ‘yan siyasa, malamai, da al’ummar yankin, wadanda suka bayyana jin dadinsu da wannan ci gaba.  

Gyaran makarantar ya hada da samar da kujeru da inganta yanayin karatu a cikin ajujuwa, gina rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, dakunan bahaya, da sauran kayayyakin more rayuwa don amfanin dalibai da malamai.  

Da yake jawabi, Manjo Janar Danja ya bayyana farin cikinsa kan kammala wannan aikin, yana mai cewa:  

"Jihar Katsina na da makarantu fiye da 3,000, kuma ba zai yiwu gwamnati ta gyara su duka a lokaci guda ba. Wannan ne ya sa na yanke shawarar farawa daga garin Danja domin tallafa wa ilimin yara."  

Ya kara da cewa: "Gyaran da aka yi ya hada da samar da rijiyar burtsatse, dakunan bahaya, da kujeru don tabbatar da ingantaccen yanayin karatu ga dalibai."

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina,  Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umaru Radda a taron, ya yaba da gudunmuwar da Manjo Janar Danja ya bayar.  

"Sojojin Najeriya ba wai a fagen yaki kawai suka kware ba, har ma da taimakon al’umma. Wannan aiki abin misali ne da ya kamata a yaba," in ji shi.  

Ya kuma yi kira ga al’ummar garin da su kula da kayayyakin da aka samar don ci gaban makarantar, tare da yin koyi da irin wannan kokari domin inganta yankunansu.

Follow Us