Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruq Lawal HCIB, ya gabatar da taron manema labarai na wata-wata a ofishinsa da ke tsohon Gidan Gwamnatin Katsina, inda ya mayar da hankali kan ci gaban da aka samu a fannin ilimi a jihar.
Malam Faruq ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta dukufa wajen inganta ilimi domin samar da ingantaccen makoma ga al’ummar jihar. Ya ce tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu, gwamnati ta zuba jari mai yawa don tabbatar da ingancin koyo da koyarwa.
A cewarsa, gwamnati ta kashe Naira biliyan 9.1 ta hannun Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina (SUBEB) domin gina sababbin ajujuwa 160, gyara 258, samar da rijiyoyin burtsatse 81, da ban daki 46, tare da gidajen malamai 20. Haka nan, an samar da kujerun malamai 612 da kujerun dalibai 14,602.
Mataimakin gwamnan ya kuma bayyana cewa an kashe Naira biliyan 5.6, karkashin shirin TIS domin gina sabbin makarantu 150 tare da samar da wutar lantarki ta hasken rana, rijiyoyin burtsatse, da kayan koyarwa na zamani.
A matakin sakandare, gwamnatin ta kashe Naira biliyan 6.8 domin gina da gyaran makarantun sakandare, samar da littattafai, kayan koyo da koyarwa, da kuma biyan kudin jarabawar dalibai. Haka nan, an gina sabbin makarantu na musamman a shiyyoyin 'Yan majalisar Dattawa guda uku, tare da gyaran makarantu kamar su GSS Ingawa da GGSS Kabomo.
Dangane da ilimin kimiyya da fasaha, Malam Faruq ya bayyana cewa an kashe Naira biliyan 1.4 wajen gina da gyaran makarantu irin su GTC Mashi da GSS Kafur. Haka nan, an bai wa malamai horo tare da samar da kayan aiki kamar kwamfutoci, Solar mai aiki da hasken rana, da motocin sa ido domin inganta koyo da koyarwa.
Bugu da ƙari, mataimakin gwamnan ya ce shirin AGILE na bunkasa ilimin ‘yan mata ya taimaka wajen gina sabbin makarantu 75, gyara wasu 578, da kuma bayar da tallafi na kudi ga dalibai ‘yan mata 4,111.
A ƙarshe, Malam Faruq Lawal ya jaddada cewa wannan kokari na gwamnatin jihar Katsina sun kawo gagarumin ci gaba a fannin ilimi, musamman wajen habaka yawan daliban da ke shiga makarantu da kuma inganta yanayin koyo a fadin jihar.