Muhammad Ali Hafizy @Katsina Times
A wani mataki na inganta tsarin ilimi a jihar Katsina, Gidauniyar Ilimi ta Jihar Katsina (Katsina State Education Fund) ta kaddamar da rabon kayayyakin karatu na musamman ga wasu makarantun jihar, wanda aka yi a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu 2025, a harabar gidauniyar dake titin Gobarau cikin garin Katsina.
Taron kaddamarwa, wanda ya samu halartar manyan jami’an gidauniyar da masu ruwa da tsaki, ya hada da Daraktan Gidauniyar, Alhaji Aliyu Balarabe Saulawa, Sakataren Gidauniyar, Alhaji Kabir Lawal Rumah, Alhaji Kabir Aliyu Maska, Alhaji Mustapha Ibrahim Zango, da kuma Marafan Katsina, wanda ya wakilci Sarkin Katsina Alhaji Dakta Abdulmumini Kabir Usman. Wannan taro ya kasance wani muhimmin mataki na tabbatar da ingancin ilimi da ci gaban makarantu a jihar.
A cikin jawabin da ya gabatar, Sakataren Gidauniyar, Alhaji Kabir Lawal Rumah, ya bayyana godiya ga Allah bisa wannan kokari na gidauniyar wajen samar da muhimman kayayyakin koyo da koyarwa ga makarantun jihar, musamman ga makarantun da ke da bukatar tallafi, makarantun masu lalurar gani da na ji. Ya ce, wannan mataki na gidauniyar yana daga cikin shirye-shiryen inganta tsarin ilimi da kuma taimakawa dalibai da malamai wajen samun ingantattun kayan aiki.
Sakataren ya yi kira ga dukkanin wadanda aka bai wa wannan tallafi da su dage wajen kokarin inganta karatunsu, tare da mai da hankali wajen yin amfani da kayayyakin karatu domin samun nasara a fannin ilimi. Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar da su shiga cikin wannan muhimmin aiki na tallafawa karatun yara, wanda zai taimaka wajen inganta tsarin ilimi a jihar.
Makarantun da suka samu wannan tallafi sun hada da makarantun masu lalurar gani, makarantun masu lalurar ji, da sauran makarantun da ke bukatar taimako na musamman wajen samar da kayan koyo da koyarwa. Kayayyakin da aka rabawa makarantu sun hada da littattafai masu inganci, kayan rubutu, da sauran muhimman kayayyaki da za su taimaka wajen inganta tsarin karatu, musamman ga daliban da ke fuskantar matsalolin rashin kayan koyo a makarantu.
A karshe, wannan mataki na Gidauniyar Ilimi ta Jihar Katsina yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tabbatar da cewa kowane yaro, ko da yana da wani lalura, yana da damar samun ingantaccen ilimi a jihar. Wannan mataki na inganta kayayyakin koyo zai taimaka wajen gina al'umma mai ilimi, wanda zai kawo ci gaba mai dorewa a jihar Katsina.