Kotu Ta Dage Gurfanar Da Tsohon Shugaban NHIS Zuwa 3 Ga Fabrairu

top-news

Mai shari’a Chinyere E. Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Kuchiako, Kuje, a ranar Alhamis, 30 ga Janairu, 2025, ta dage gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, tsohon Sakatare Janar na National Health Insurance Scheme (NHIS), zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025.  

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama Farfesa Yusuf a ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025, tare da gabatar da shi gaban kotu a ranar Alhamis, 30 ga Janairu, 2025*l, domin gurfanar da shi kan zarge-zargen zambar kuɗi.  

Sai dai kotu ta dage shari’ar zuwa ranar Litinin, 3 ga Fabrairu, 2025, domin bai wa masu gabatar da ƙara damar gyara tuhume-tuhumen da ake masa.  

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, Isah Dokto Haruna, wanda ya wakilci babbar lauyan kariya, O.I. Habeeb (SAN), ya gabatar da buƙatar beli ga wanda ake tuhuma, amma kotu ta yi watsi da roƙon nasa saboda dage gurfanarwar.  

Mai shari’a Nwecheonwu ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025, tare da bada umarnin ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a hannun EFCC har zuwa lokacin da za a sake gurfanar da shi.  

Farfesa Usman Yusuf na daga cikin Dattawan Arewa da yayi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Follow Us