Ingancin Tsaro: Harkokin Koyo Da Koyarwa Sun Fara Kankama a karamar hukumar Danmusa

top-news

Sannu a hankali harkokin koyo da koyarwa na dawowa kamar yadda suke a da akaramar hukumar Danmusa Bisa samun saukin Rashin tsaro da ake samu a yankin

Sakataren ilimi na karamar hukumar Danmusa ya bayyana cewa makarantu 25 daga cikin 34 da suke a kulle sakamakon kalubalen tsaro da ya addabi Yan'kin aka sake budewa a halin yanzu.

Alhaji zaharadden Umar Danmusa ya bayyana haka a lokacin da  ya jagoranci wata tawagar yan'jarida zuwa ziyarar duba makarantun karamar hukumar.

Ya bayyana cewa sun hade sauran makarantu 11 da suka rage a wurare guda don saukakama malamai da dalibai.

Sakataren ilimi ya alakanta nasarar sake bude makarantu da kokarin gwamnati mai ci yanzu wajen yaki da matsalar tsaro.

Alhaji zaharadden Umar Danmusa ya jaddada cewa hakan manuniya ce karara bisa irin kokarin gwamna Radda a yaki da kalu balen tsaro, da kuma tabbatar da cewa ya'yan masu karamin karfi sun samu ingantaccen ilimi.

Ya kuma yabama gwamna Radda bisa nada Dr. Kabir Magaji Gafiya a matsayin shugaban hukumar ilimi bai daya ta jahar katsina a matsayin wanda  ya dace.

Alh Zaharaden Umar Danmusa yayi kira ga Al'umma da a cigaba da addu'a don samun dawamammen zaman lafiya a jihar katsina da cigaba.

Da suke jawabi shuwagabannin makarantun primare na Mara A  malam Ali almu dana Yarima  pilot Danmusa ya'u Sada sun yabama sakataren ilimi na Karamar Hukumar bisa kokarin shi na bunkasa ilimi a Yan'kin,
Sun kuma bayyana godiyar su ga gwamnatin jiha bisa kokarinta na maido da zaman lafiya a Yan'kin.

Wata daga cikin malamar wucin gadi malama Binta  da aka zanta da ita ta roki gwamnatin jiha data taimaka ta dauke su malamai na din din-din.

Ana shi bangaren Dan galadiman mara  muhamd Abdullahi da yayi jawabi amadadin iyayen yara ya godema Sakataren ilimi na Karamar Hukumar Alh zaharaden Umar Danmusa bisa kokarin shi wajen bunkasa ilimi.

Follow Us