Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kurfi da Dutsinma Ya gudanar da Ziyarori a yankin
- Katsina City News
- 27 Jan, 2025
- 52
Muhammad Ali Hafiziy, Katsina Times
A ranar Asabar 25 da 26 ga Janairu, Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Kurfi da Dutsinma, Hon. Aminu Balele Ɗan Arewa, ya kai ziyara ta musamman a garuruwan Kurfi da Dutsinma domin inganta harkokin addini a ranar Asabar, 26 ga watan Janairun 2025.
A garin Dutsinma, Hon. Aminu ya gana da dalibai da malamai a makarantar Islamiyya ta mata, inda ya shaida musu cewa zai dauki nauyin kuɗin makarantar su na tsawon shekara guda. Har ila yau, ya bayyana wasu sabbin hanyoyi da za su taimaka wajen inganta karatun addini da walwalar daliban.
A yayin ziyarar, Hon. Aminu ya gana da limamai da ladanai na yankin, inda ya yi alkawarin ƙarin alawus domin ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukan addini da kuma sanya Najeriya gaba ɗaya cikin addu’o’in alheri.
Daga bisani, Ɗan Majalisar ya halarci jana'izar babban yaron sa, Shamsu Kata, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a garin Kurfi. Wannan al'amari ya girgiza al'umma tare da jawo addu'o'i na fatan rahama ga mamacin.
Wannan ziyara ta nuna jajircewar Hon. Aminu wajen inganta rayuwar al'ummarsa tare da bayar da muhimmanci ga harkokin addini da jin daɗin jama'a.