Hukumar Hisbah Ta Jihar Katsina Ta Ziyarci Kamfanin Jaridar Katsina Times
- Katsina City News
- 22 Jan, 2025
- 42
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2025, Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, karkashin jagorancin Mataimakin Kwamanda, Dr. Ibrahim Iyal Gafai, ta kai ziyara ta musamman zuwa Kamfanin Matasa Media Links. Kamfanin da ke wallafa Katsina City News Magazine, Katsina Times, da kuma jaridar yanar gizo ta Taskar Labarai.
Ziyarar ta kasance don karfafa dangantaka da inganta hadin gwiwa tsakanin sassan biyu a kokarin su na yi wa al’umma hidima.
Da yake jawabi a madadin hukumar, Mataimakin Kwamanda, Dr. Ibrahim Iyal Gafai, ya bayyana cewa wannan ziyara wani bangare ne na manufofin Hukumar Hisbah na kara kulla dangantaka mai kyau da gabatar da ma’aikatan hukumar ga tawagar Katsina Times. Ya ce, “Ko da yake muna da kyakkyawar alaka mai tsawo da wannan kamfani da Babban Edita Malam Muhammad Danjuma Katsina, mun zo ne don kara sada zumunci da girmama juna.”
A nasa jawabin, Babban Editan Katsina Times kuma Shugaban Kamfanin Matasa Media Links, Malam Muhammad Danjuma Katsina, ya nuna godiya ga hukumar tare da yaba wa ayyukansu. Ya bayyana Dr. Ibrahim Iyal Gafai a matsayin ƙane, yana mai cewa akwai kusanci tsakaninsu da ya wuce zuwa dangantaka ta iyaye. Har ila yau, ya yaba wa Babban Kwamandan Hukumar, Dr. Aminu Usman (Abu Ammar), yana mai cewa ya san shi tun kafin a kafa hukumar Hisbah.
Danjuma Katsina ya tabbatar wa hukumar cewa kamfanin jaridar zai ci gaba da tallafa wa manufofinsu masu kyau. Ya ce, “Na umarci ma’aikatana da su mayar da hankali wajen yada kyawawan ayyukan hukumar Hisbah, tare da bada muhimmanci ga kashi 90 cikin dari na ayyukan su.”
Sai dai ya ja hankalin hukumar da sauran jama’a cewa kafar yada labarai na da matsayi na tsaka-tsaki wajen bauta wa al’umma. “Dukkan wata kafar yada labarai aikin ta shi ne yi wa al’umma hidima. Duk da cewa muna da kyakkyawar alaka, aikinmu na fitar da rahotanni na gaskiya da daidaito wani lokacin zai sa mu buga labarai da ba kowa zai so ba. Wannan ba yana nufin rashin alaka bane, sai dai kira ne ga gyara da ci gaba,” in ji shi.
Ya kuma bukaci hukumar da ta rika yin hadin kai tare da kafar yada labarai, yana mai cewa, “Idan mun yi kuskure, ku sanar da mu ku bamu shawara ko nasiha, don mu gyara. Haka kuma, idan muka samu rahoto da ke dauke da korafi akan hukumar ku, zamu tuntube ku don jin karin bayani don tabbatar da daidaito a rahotonmu.”
A karshe, Babban Editan ya yi fatan alheri ga Hukumar Hisbah a madadin Katsina Times da ma’aikatanta.
Wannan ziyara ta kasance wata dama ta karfafa hadin kai da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu. Abin lura ne cewa Katsina Times ce kafar yada labarai ta farko da ta fallasa wasu bidiyoyin sirri da ke nuna yadda ake aikata miyagun dabi’u a Jihar Katsina kafin kafa hukumar Hisbah. Jaridar ta kasance mai sadaukarwa wajen yaki da dabi’u marasa kyau tare da inganta rayuwar al’umma.