Gidauniyar Hadin-kan Funtua Ta yi Alkawarin Inganta Ilimi, Kiwon lafiya da sauransu
- Katsina City News
- 21 Jan, 2025
- 73
Wata gidauniya Mai suna Funtua Unity Foundation ta sha alwashin hada gwiwa da gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan kasuwa da kuma sarakunan gargajiya domin samar da ci gaba mai dorewa a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.
Shugaban gidauniyar, Kwamred Mannir Suleiman, ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci sauran ‘ya’yan kungiyar zuwa ziyarar ban girma ga Sarkin Maskan Katsina Hakimin Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, a fadarsa da ke Funtua.
Kwamared Mannir Suleiman ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali ne kan muhimman fannoni guda bakwai da suka hada da hadin kai, da ilimi, da samar da aikin yi, da bunkasa sana'o'i, da inganta harkar kasuwanci, da sa ido kan jami'an gwamnati, da kuma hada gwiwa da kungiyoyi don habbaka tattalin arzikin karamar hukumar Funtua.
Ya ce gidauniyar za ta bunkasa ilimi da ci gaban rayuwar yara da matasa domin su zamo masu dogaro da kai.
Kwamared Suleiman ya ce har ila yau gidauniyar za ta hada hannu da fitattun ’yan asalin garin Funtua wajen samar da guraben aikin yi a matakin jiha da tarayya ga wadanda suka kammala karatu a manyan makarantu da kuma samar da jarin kasuwanci ga matasa.
Ya shuwagabannin gidauniyar sun Kai ziyarar a fadar Sarkin Maska ne domin nada shi a matsayin Urban gidauniyar da kuma neman albarkarsa tare da rokonsa da ya yi amfani da mukaminsa wajen karfafa aiyukan gidauniyar.
A nasa jawabin, Hakimin na Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, ya amince da zama uban gidauniyar, ya kuma yaba da hangen nesan wadanda suka assasa ta.
Ya bayyana gidauniyar a matsayin abin farin ciki musamman a daidai lokacin da Funtua ke fuskanci kalubale da dama na zamantakewa da tattalin arziki.
Ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya da hadin kai ga gidauniyar tare da hada kai da shugabanninta domin cimma manufofinta.