Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Ya Jaddada Aniyar Tabbatar Da Doka Da Oda, Tare da Jajircewa Wajen Rikon Amana

top-news

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa tabbatar da doka da oda na buƙatar ƙwarewa ta fasaha, jajircewa da kuma gaskiya da riƙon amana.

A ranar Litinin ne gwamnan ya kasance babban baƙo a wajen taron shari'a na shekara-shekara ta 2024 da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) reshen Gusau ta shirya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa a yayin taron, gwamna Lawal ya samu lambar yabo ta karramawa a matsayin babban abin tunawa kuma mutum mai tasiri ga al’ummar jihar Zamfara.

Ya ƙara da cewa, shugaban NBA reshen Gusau Mu'azu Shehu Ahmad Esq ne ya ba gwamnan lambar yabon.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa taro kamar na NBA yana ƙara ƙwarin gwiwa ga ƙwararrun lauya don musayar ra'ayoyi da inganta samar da adalci, dimokuraɗiyya, da bin doka.

Ya ce, "Taken taron na bana shi ne; "Tabbatar da Doka: Ginshiƙin Ci gaban Dimokraɗiyya". Yana nuna da irin rawar da fannin shari’a ke takawa wajen tsara al’ummarmu ta hanyar tabbatar da kyawawan ɗabi’u, adalci da riƙon amana.

“Ina da yaƙinin cewa za mu iya ƙarfafa ginshiƙin dimokuraɗiyyar mu da kuma ginshiƙin wanzuwar mu a matsayin al’umma ta hanyar sadaukar da kai ga bin doka da oda.

“A halin da ake ciki, ina yaba wa Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya reshen Gusau, bisa namijin ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da adalci da bin doka da oda. Haƙiƙa sadaukarwar da kuka yi ga wannan aiki mai daraja abin a yaba ne kuma abin koyi ne.

“Ina kira gare ku da ku ci gaba da nuan halin ƙwarai na ma’aikatan shari’a don tabbatar da cewa kun kasance ginshiƙin fata ga talakawa da duk masu neman adalci.

“Na yaba wa ƙoƙarin lauyoyi wajen ganin an yi adalci ba tare da nuna son kai ba cikin gaggawa, har a lokutan da ake fuskantar ƙalubale. Tsayuwarku ta kasance ƙwarin gwiwa kuma ta zama abin tunatarwa cewa adalci shi ne ginshiƙin kowace al'umma mai wayewa.

“Gwamnatin jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Muna aiki tuƙuru don magance matsalolin rashin tsaro da samar da yanayin da al’ummarmu za su zauna ba tare da tsoro ba.

“Ina kuma so in jaddada muhimmancin ilimin shari’a wajen ƙarfafa tsarin adalcinmu.

“Tsarin ilimin shari'a yana buƙatar karatu da haƙiƙa. Ina roƙon ku da ku riƙa amfanar juna wajen da horo da ilimin da ku ka samu, kamar wannan taro na makon shari'a, don kasancewa a sahun gaba wajen aiki da doka.

“A wannan lokaci, ina miƙa godiya ta ga waɗanda suka shirya wannan babbar lambar yabo a gare ni. Jajircewar da na yi na yaƙar rashin tsaro, da bin doka da oda, da gina ababen more rayuwa abin a yaba ne matuƙa.

“Ba abin alfahari ba ne kawai, a’a, shaida ce ga namijin ƙoƙarin da duk waɗanda suka yi aiki tare da ni suka yi wajen gina jihar Zamfara mai tsaro, da adalci, da wadata cikin watanni 20 da suka gabata.

“A ƙarshe, yayin da nake yaba wa Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen Gusau, kan yadda suka saba shirya wannan taron na shekara-shekara, cikin alfahari nake bayyana buɗe makon taron shari'a na 2024. Ina addu'ar shawarwarinku su kasance masu ma'ana da tasiri. Allah Ta’ala Ya yi mana jagora a cikin ayyukanmu baki ɗaya”.