'YAN SANDA NA BINCIKEN RIGISTARA DA MATAIMAKIN BASA NA KATSINA INSTITUTE OF TECHNOLOGY AND MANAGEMENT STUDIES.
- Katsina City News
- 14 Sep, 2023
- 940
@ katsina times
Rundunar yan sanda ta jahar katsina na binciken mataimakin basa, Murtala Iliyasu da rijistara shamsudden Ahmed na makarantar ''katsina institute of technology and management studies" akan zargin amfani da wata kungiyar da bata da rijista da juya takardun gwamnati don bata sunan shugaban makarantar Dakta Babangida Albaba.
Binciken ya samo asali ne, a bisa wani koke da shugaban makarantar Dakta Babangida Albaba ya shigar ga hukumar yan sanda akan cewa wasu da bai San kosu wanene ba, suna amfani da sunan wata kungiya mai suna "katsina watch"" suna bata masa suna.
Dakta Albaba ya nemi da hukumar yan sanda ta binciko domin gano ko su wanene da kwatar masa hakkin sa.
Hukumar yan sanda ta Dade tana bincike, amma ta fara samun bakin zaren ne, bayan wata jarida ta wallafa zarge zarge da lambar wayar daya daga cikin Wanda ake zargin yayi rubutun.
Yan sanda sunyi amfani da kwarewarsu,ta bin sakon waya,inda suka gayyaci Babban wanda ake zargin shine mataimakin basa na makarantar Murtala Iliyasu, daga baya suka gayyaci rijistara na makarantar.shamsudeen Ahmed
Zargin ya hada harda wani tsohon rijistara na makarantar da ya bari.wanda shima yan sanda sun gayyace shi amma baya gari.
Majiyar mu a hukumar yan sanda ta tabbatar mana da binciken da kuma gayyatar wadanda ake zargi.
Majiyar a hukumar yan sanda tace suna akan bincike, basu kammala ba.
Masana sanin aikin gwamnati daga ciki har da tsaffin shugabannin ma aikata( head of service)na jahar katsina guda biyu sun ce Babban laifi ne, ma aikaci ya Boye bayan kungiyar karya yana murguda bayanan ofis da yake don bata sunan shugaban sa.
Suka ce, dokar aiki ta bayar da hanyoyi na hukunta na kasa da kai ko sama da kai in kaga yana abin da ba dai dai ba.ko kana zargin shi da yin ba dai dai ba.
Lauya a gidan lauyoyi na Hikima and co Abuja,Batista shehu Danladi ya fada ma jaridar katsina times cewa,zargin aikita abin da yan sanda ke binciken Maaikatan makarantar, na iya kaisu ga shekaru a gidan yari idan kotu ta same su da laifi.
Barista shehu yace, domin zargin ya hada da sojan gona na amfani da kungiyar karya,da cyber crime na amfani da yanar gizo don bata suna.da bata suna da kuma cin amana aiki da ta kasa.
Wata kungiya marubuta da mashaharta wadda ke da rijista da gwamnatin jaha mai suna katsina books clubs tayi alwadai da hallayyar ma aikaci, Wanda bai iya fitowa gaba da gaba ya fuskanci zalunci in ya tabbatar anayi, sai ya Boye a bayan rubutun sharri da Boye suna.
Kuma tayi Kira ga gwamnan katsina Dakta umar Radda yayi hankali da irin wadannan matsoratan Maciya amana.
Katsina books club suka ce,in kana da zargi kana iya baiwa jami an tsaro a rubuce su bincika,ko ka baiwa amintattun kwararrarun yan jaridu suyi bincike na adalci su bayyana ma duniya.
A shekarun baya,lokacin mulkin Masari anyi lokacin da wasu ma aikatan gwamnatin katsina suka rika baiwa Mahadi shehu takardu da bayanan karya akan gwamnatin,shi kuma yayi ta bidiyo da takardun.Maganar da har yanzu tana Babbar kotun tarayya dake Kano.
Wannan shine zargi na farko ga wasu ma aikatan gwamnati tunda wannan sabuwar gwamnatin ta hau.
Katsina times
Www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
Www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762