Kungiyar Tsofaffin Sakatarorin PDP ta K34 Ta Jaddada Goyon Bayanta ga Tafiyar Dikko Project Movement
- Katsina City News
- 20 Jan, 2025
- 93
Kungiyar Tsofaffin Sakatarorin PDP ta K34 Ta Jaddada Goyon Bayanta ga Tafiyar Dikko Project Movement
Kungiyar tsofaffin sakatarorin PDP ta lokacin K34 ta bayyana cikakkiyar mubaya’arsu ga shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Hon. Musa Gafai, domin bayar da gudunmawa ga nasarar Gwamna Dikko Umar Radda a zaɓen 2027.
Shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Hon. Musa Gafai, ya gana da tsofaffin sakatarorin PDP na ƙaramar hukumar Katsina a ranar Lahadi, 19 ga watan Janairu, 2025, karkashin jagorancin Alhaji Sani Yakubu Kofar Guga. Wannan taro ya gudana ne da nufin kulla dangantaka mai ƙarfi da tabbatar da haɗin kai tsakanin Dikko Project Movement da kungiyar tsofaffin sakatarorin PDP, wanda aka fi sani da Ex-Secretary PDP Forum.
A jawabin Hon. Musa Gafai, ya yaba da irin gagarumar gudunmawar tsofaffin sakatarorin PDP a harkar siyasa tun daga shekarun 1990 a lokacin K34, tare da nuna farin cikinsa kan yadda suka nuna goyon bayansu ga manufofin Gwamna Dikko Radda da kuma kudurinsu na bayar da tallafi wajen cimma nasarar tafiyar siyasar jihar Katsina.
A nasa ɓangaren, shugaban kungiyar Ex-Secretary PDP Forum, Alhaji Sani Yakubu Kofar Guga, ya bayyana cewa kyawawan manufofin Gwamna Dikko Radda, musamman ayyukan alherin da yake aiwatarwa a fadin jihar Katsina, sun ja hankalinsu har suka yanke shawarar sake shiga cikin harkokin siyasa bayan tsawon shekaru takwas da suka ja baya.
Kungiyoyin biyu sun jaddada kudirinsu na yin aiki tare wajen dawo da mutanen da aka rasa, kulla alaƙa mai ƙarfi a siyasance, da kuma ƙirƙirar tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’umma. Wannan haɗin gwiwa na nufin tabbatar da nasarar Gwamna Dikko Umar Radda a zabukan da ke tafe.