An Daura Auren 'Ya'Yan Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan Katsina, Sanata Yakubu Lado Danmarke
- Katsina City News
- 17 Jan, 2025
- 67
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, tare da manyan baƙi, sun halarci daurin auren 'Ya'yan Tsohon Dantakarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar PDP na shekarar 2023 Sanata Yakubu Lado Danmarke
An gudanar da wannan gagarumin Daurin Aure a Masallacin Bani Coomasie, GRA, Katsina, bayan sallar Juma’a.
Wannan bikin Daurin Aure ya tattaro fitattun mutane daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da manyan ‘yan siyasa, attajirai, 'Yan'uwa da Abokanan Arziki, Daga cikin waɗanda suka halarci wannan Daurin Aure akwai, Sanata Abdul Ningi, dan majalisar dattijai daga Arewa maso Gabas, Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa, wanda ya kasance daya daga cikin jiga-jigan siyasar yankin kuma wakilin ango, Alhaji Dahiru Mangal, shahararren attajirin a Najeriya kuma wakilin amaren gaba dayan su uku.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, wakilin ango, Sanata Kabiru Gaya, tsohon gwamna kuma tsohon dan majalisar dattawa daga jihar Kano, tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa, tsohon Gwamnan jihar Sokoto Aminu waziri tambuwal, 'Yan majalisar dokokin tarayya da na jiha duk sun samu halartar gagarumin Daurin Auren.
Wannan Daurin Aure ya zamo wata babbar dama ta haɗuwa tsakanin manyan 'Yan siyasa mabanbanta jam'iyyu a Najeriya.
A yayin da ake gudanar da bikin, an gabatar da addu’o’i na musamman domin neman albarka ga ma’aurata, tare da rokon Allah ya albarkaci rayuwarsu da zaman lafiya da samun zuri’a ta gari.