Gwamnatin taraiya ta yi wa Sarki Sanusi martani bisa kalaman sa na cewa ba zai taimaka mata ba
- Katsina City News
- 16 Jan, 2025
- 144
Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan kalaman Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II na cewa ba zai taimaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba wajen gyara manufofin gwamnatin da ke shafar ‘yan kasa.
Sanusi ya jawo cece-kuce a jiya Laraba a Legas a matsayin shugaba a taron lakca na tunawa da Gani Fawehinmi karo na 21.
A cewar Sarkin, ba zai taimaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba saboda “ba su ɗauke shi a matsayin aboki ba.”
Sai dai a yau Alhamis, Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, a cikin wata sanarwa, ya ce gwamnatin tarayya ba ta bukatar shawara da ga Sarki Sanusi wajen aiwatar da 'manufofinta masu kyau'.
Ya nuna rashin jin dadinsa cewa sauye-sauyen da masana tattalin arziki na duniya, har da shi Sarkin amma ya zu ya na kumshe su saboda wani ra'ayi na sa.
Idan aka yi la’akari da tarihin Sanusi a fannin tattalin arziki, ministan ya ce Sarkin yana da wani nauyi na musamman na bayar da gudunmawa mai inganci, maimakon kawo cikas ga sauye-sauyen da ake yi na samun ci gaba kawai saboda ya na jin haushin wasu “abokansa” a gwamnati.