Tarihin Yadda Aka Kashe Firimiya Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa 15/1/1966.

top-news

Kamar yanda a kudu maso yammacin Najeriya Captain Emmanuel Nwobosi ya jagoranci juyin mulki, a yankin arewa Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, haka ma a yankin Legas wanda yake matsayin birnin tarayyar Najeriya a wancan lokacin, Manjo Emmanuel Arinze Ifeajuna ne ya jagoranci juyin mulkin.

Tun da farko dai, Ifeajuna, Okafor da Ademoyega (Wanda Bayarbe Ne) su ne sojojin da suka shirya dukkanin dabarun yanda za’ayi a kifar da gwamnatin farar hula ta Jamhuriya Ta Farko.

Tun farko ruwayoyin tarihi sun nuna cewa ministan harkokin cikin gida na jamhuriyar ta farko, Alhaji Shehu Usman Shagari, ya sha sanarwa da Tafawa Balewa shirin sojojin nayin juyin mulki. Akwai ranar da ma sai da ran firaministan ya ɓaci sosai akan maganar yace wa Shagari kada ya ƙara tayar masa wannan maganar idan bayason ganin ɓacin ran sa. A lokacin Gwamnatin ba ta ma yadda cewa akwai shirin juyin mulkin ba.

Dai-dai misalin ƙarfe biyu da ƴan wasu mintina, na Ranar 15 Ga Watan Junairu 1966 wasu sojoji ƙarƙashin jagorancin Manjo Ifeajuna suka dira Gidan Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa dake titin King George a birnin Legas. (A lokacin Legas Shi ne Babban Birnin Kasa).

Zuwan nasu ya faru ne awanni kaɗan bayan Tafawa Ɓalewa ya kammala tattaunawa da wasu daga cikin ministocin sa waɗanda suka haɗa da K.O. Mbadiwe ministan harkokin kasuwanci, Raymond Njoku ministan harkokin sadarwa da kuma Taslim Elias babban lauyan gwamnatin tarayya.

A lokacin da suka shiga gidan sun fafata da jami’an ƴan sanda da suke gadin gidan amma basu kashe kowa a cikin su ba. Bayan shigar su cikin Gidan babban abokin Tafawa Balewa kuma surukin sa Madakin Bauchi na wancan lokacin, Alhaji Abubakar Garba, yana cikin Gidan amma basu gan shi ba.

Daga baya har Madakin Bauchi yake cewa wanda ya jagoranci far ma gidan Tafawa Balewa ba Manjo Ifeajuna bane da ake faɗa, Manjo Okafor ne saboda a cewar Madakin Bauchin wanda ya kalla da idon sa wani soja ne fari siriri mai gashin baki, to amma dukkanin waɗannan siffofin na Manjo Ifeajuna ne. Daga baya dukkanin bincike sun tabbatar da Ifeajuna ne jagoran tafiyar ba Okafor ba.

Bayan Manjo Ifeajuna da tawagarsa sun shiga gidan sun yi barazanar harbe masu hidimai na musamman ga Tafawa Balewa watau ADCs ɗinsa guda biyu masu mukamin Kaftin wanda dayan su ya kasance dan arewacin Najeriya, da kuma Maxwell ɗan ƙabilar Ibo, idan har basu nuna musu gurin da Tafawa Ɓalewa yake ba. Da farko sun turje sun ce su sam ba su san yanda firaministan yake kwana ba kuma basu da makullan ɗakin kwanan sa. Amma daga karshe da kowanensu aka ɗora masa bindiga a ka ana faman matsa kunamar, sai suka wuce sama kai tsaye wajen da Tafawa Balewa yake kwana. Suka ƙwankwasa masa ƙofa. Yana buɗe wa yaga Manjo Ifeajuna tsaye ya shuno masa bindiga kai tsaye.

Da ganin Manjo Ifeajuna tsaye cikin wannan yanayin, firaminista ya tambaya shin lafiya kuwa. Ifeajuna yayi masa sarawar ban girma kuma ya sanar dashi yazo ya kamashi ya tafi dashi ne. Tafawa Balewa yace to kafin a tafi dashi yana roƙon alfarma a bashi dama yayi sallah kuma ya canja kayan jikinsa. Aka bashi dama yayi sallah ya saka farar riga da farin wando da kuma takalmi silifa.

Ana ƙoƙarin fita dashi hadiminsa ɗan arewa, kaftan, ya roƙi su ifeajuna cewar su taimaka kada su tafi da Tafawa Balewa saboda shi kadai ne ɗan mahaifiyarsa kuma ta tsufa sosai wani abu yana faruwa dashi zuciyar ta za ta iya samun matsala. Amma duk da wannan roƙo basu ji ba suka wuce da shi zuwa ƙasa.

Tafiya da Tafawa Balewa, Kaftin ya biyo su har kan titin da suka ajiye motar su yana ta basu baki akan su faɗa masa dalilin tafiya da Tafawa Balewa kuma ina zasu je dashi idan sun tafi dashi me zasu yi masa. Ya cigaba da yi musu magiya har sai da Tafawa Balewa da kansa ya dakatar dashi ya kuma umarce shi cewa ya koma gida.

Suka tafi dashi zuwa kan titi suka umarce shi da ya shiga cikin motar su ta sojoji kuma suka tabbatar masa da cewa ba zasu cutar dashi ba saboda sun san dukkanin rikice-rikicen siyasa da suke faruwa a ƙasar musamman a yankin kudu maso yamma ba laifin sa bane. Daga nan suka bi kan titin Awolowo suka tafi.

Bayan tafiya da firaminista, ma’aikatan gidan sa sun yi gaggawar ƙiran Kwamishinan ƴan sandan birnin Legas Hamman Maiduguri suka sanar da shi an sace Tafawa Balewa. Suka sake kiran shugaban rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar Aguyi Ironsi suka sanar mashi halin da ake ciki.

Bayan kiran Hamman Maiduguri, shi kuma ya kira shugaban rundunar ƴan sanda Najeriya watau Alhaji Kam Salim wanda shi ma yake a birnin Legas. Daga nan, tsakanin ƙarfe 3 na dare su biyun suka wuce ofishin mataimakin babban magatakardan ma’aikatar tsaro watau Alhaji Ahmadu Kurfi domin su sanar da shi abinda yake faruwa.

A lokacin da abin ya faru ma’aikatar ta tsaro tana hannun babban magatakardan ta Alhaji Suke Kolo saboda Ministan harkokin tsaron Alhaji Inuwa Wada baya nan.

Bayan labari ya fita cewar an sace firaminista an kuma kashe wasu daga cikin manyan sojoji, musamman wadanda suka fito daga arewa, shugaban rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar Aguyi Ironsi ya haɗa bataliya ta biyu domin su shawo kan matsalar masu juyin mulkin kuma a kama su.

A lokacin da suka samu labarin Aguyi Ironsi yana gari kuma ya shirya tsaf domin tunkarar su, daga nan sai suka fara tunanin yanda zasu tsira. Tun lokacin da suka ɗauko Tafawa Balewa daga cikin gidan sa, yana cikin motar su ta sojoji har ya zuwa wannan lokacin ana ta zagayawa gurare dashi. A kan idon sa an kashe sojoji da dama.

Kisan Abubakar Tafawa Balewa.

Suna cikin tafiya da firaminista sai aka wuce asibitin sojoji na Yaba domin a duba lafiyar Leftanen Ezedigbo saboda raunuka da ya samu sakamakon arangamar sa da masu gadin gidan Janar Maimalari lokacin da suka je kashe shi. Bayan Ifeajuna ya ajiye Ezedigbo a asibiti, sai suka wuce titin Abeokuta da Tafawa Balewa a cikin motar.

Lokacin da suka hau hanyar Legas zuwa Abeokuta sai Manjo Ifeajuna ya cewa Firaminista ya sauka a motar. Yana fita ya harbe shi ya faɗi ƙasa. Bayan faɗuwarsa sai Manjo Okafor yaje ya bincika gawar ya tabbatar Tafawa Balewa ya mutu sai suka buɗe bayan motar su suka fito da gawar Leftanen kanel Largema suka jefar da ita kusa da ta Firaminista suka wuce hanyar garin Abeokuta.

Akan hanyarsu ta zuwa Abeokuta suka tsaya wasu sojoji guda biyu suka sauka suka koma Legas. Shi kuma Manjo Ifeajuna da abokin aikin sa Okafor suka wuce garin Enugu.

Suna isa garin suka je suka samu firimiyan yankin Inyamurai watau Dr Michael Okpara sukayi wata kwarya kwayar tattaunawa dashi wanda daga nan ne suka tafi suka ɓuya. Daga baya Manjo Ifeajuna a hankali da taimakon abokinsa Christopher Okigbo ya sulale ya gudu kasar Ghana kuma ya samu tarba ta musamman daga shugaban ƙasar Ghana na wancan lokacin Kwame Nkurumah.

Nkurumah ya bashi gida sun zauna tare da Samuel Ikoku tsohon magatakartan jam’iyyar AG ta Yarabawa wanda ya gudu ƙasar Ghana lokacin da akayi shari’ar Awolowo bisa laifin yunkurin juyin mulki a shekarar 1962.

Gano Gawar Tafawa Balewa

Har bayan kwana uku da kashe Tafawa Balewa ba a samu gawarsa da na wasu manyan sojoji ba, hakan yasa Aguyi Ironsi ya sanar wa ƴan kasa cewar har yanzu ba a san in da firaminista yake ba amma ana nan ana dubawa.

Bayan kwana biyu da yin wannan sanarwar, wani dan sandan arewa mai suna Ibrahim Babankowa mai matakin mataimakin sufartanda, ya je asibiti domin ganin likita. Yana zaune sai yaji wasu mutane suna magana akan wani irin mummunan wari mai ƙarfin gaske da suke ji a kusa da inda suke rayuwa.

Babankowa ya tambaye su suka sanar masa wajen shi ma kuma sai ya tuna akwai lokacin da yana bakin aiki rundunar sojoji sun zo sun wuce ta inda yake zuwa can wajen.

Babankowa ya ɗauki rundunar ƴan sanda suka tafi wajen domin duba abinda yake faruwa wanda isar su ke da wuya suka tarar da gawarwakin mutane guda biyu har sun fara zagwanye wa.

Ɗaya da kayan sojoji wanda aka tabbatar da ko shakka babu Leftanan Kanel Largema ne; wanda aka jefar da gawarsa kusa da ta firaministan lokacin da aka kashe shi.

Ɗaya gawar kuma ta Tafawa Balewa ne amma idan ba domin kayan da suke jikinsa ba wanda aka tabbatar sune a jikinsa lokacin da aka tafi dashi to da babu wanda zai iya gane gawarsa saboda yadda ta ɓaci.

Daga nan Babankowa ya umarci ƴan sandan da suke wajen cewar su tsaya su kula da wajen zaije ya dawo. Lokacin da Babankowa ya tafi ya sanarwa da duk wani mai ruwa da tsaki cikin harkar tsaron Najeriya cewar an gano gawar firaminista.

Kafin ya sanarwar shugaban ƙasa Ironsi kam shi ne ma ya kira shi yake tambayar sa cikin yaren Hausa shin dagaske ya gano gawar Tafawa Balewa yace tabbas haka ne.

Suka tafo zuwa wajen da gawar take suka samu waɗannan ƴan sandan da Babankowa ya bari a wajen suna nan suna jiran su.

Bayan sun iso wajen aka fara maganar jana’izar firaministan amma babban abokinsa Madakin Bauchi yace lallai Bauchi za a dawo da gawar domin ayi masa sutura.

Jana’izar Tafawa Balewa

Haka kuwa aka yi, Madakin Bauchi ya bawa Kaftan umarnin cewa ya je ya sanarwa matan Tafawa Balewa; Hajjiya Jummai da Hajjiya Laraba abinda yake faruwa kuma su shirya tafiya Bauchi.

Daga nan aka ɗauki gawar aka wuce da ita filin jirgin Ikeja. Kwamishina ƴan sanda Legas, shugaban rundunar ƴa sandan ƙasa, mataimakin shugaban rundunar ƴan sanda, ministan harkokin tsaron, Madakin Bauchi da ministan albarkatun kasa da makamashi Alhaji Yusuf Maitama Sule su ne suka raka gawar Tafawa Balewa zuwa birnin Bauchi kuma sun isa ne ranar bikin sallar azumi saboda duk abubuwan da suka faru lokacin juyin mulkin, sun faru ne cikin azumin watan Ramadan.

Daga nan aka yiwa gawar sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Muhammad Sesey