Shugaban Kwamitin Sanya Ido A Kan Ayyukan Samar da Ruwan Sha a Jihar Katsina Ya Jaddada Muhimmancin Tabbatar da Ingancin Ayyuka
- Katsina City News
- 14 Jan, 2025
- 91
Daga Abbas Nasir, P.R.O (STOWASSA)
Shugaban Kwamitin Sanya Ido A Kan Ayyukan Samar da Ruwan Sha, Alhaji Rabi'u Gambo Bakori, ya gudanar da taro na musamman tare da mambobin kwamitin domin tabbatar da ci gaban ayyukan samar da ruwan sha a shiyyoyin yan majalisa dattawa uku na jihar Katsina. Taron ya gudana a dakin taro na hukumar STOWASSA, dake cikin Garin Katsina.
Aikin samar da ruwan sha zai gudana a kananan hukumomi bakwai da ke cikin shiyyoyin yan majalisa dattawa uku, da nufin samar da ruwan sha mai tsafta a matsakaitan birane, wanda ya zama wani bangare na kudirin gwamnatin jihar Katsina.
A cikin jawabin da ya yi wa mambobin kwamitin, Alhaji Rabi'u Gambo Bakori ya bayyana cewa babban manufa na kwamitin shi ne sanya ido kan ayyukan samar da ruwan sha a yankunan, don tabbatar da cewa an aiwatar da su yadda ya kamata da inganci.
Ya sha alwashin daukar matakan da suka dace domin tabbatar da nasarar wannan shiri, wanda zai inganta rayuwar al'umma a jihar Katsina.
Alhaji Rabi'u Gambo Bakori ya kuma yabawa shugaban hukumar STOWASSA, Alhaji Ibrahim Lawal Dankaba, bisa kwarewa da dattako da yake nunawa wajen jagorantar hukumar. Ya yi kira ga masu rike da mukamai na siyasa su yi koyi da irin tallafin da shugaban hukumar ke bayarwa ga gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda PhD wajen ciyar da jihar Katsina gaba.
A karshe, shugaban kwamitin ya yabawa Gwamna Radda bisa nadin Alhaji Ibrahim Dankaba a matsayin shugaban STOWASSA, tare da fatan cewa zai sauke nauyin da aka dora masa cikin nasara. Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta ci gaba da bunkasa ayyukan raya kasa domin inganta jin dadin al'ummarta.