EFCC Ta Kama Jami’ai Biyar Na Hukumar Haraji Ta Katsina Kan Zargin Satar Naira Biliyan N1.3
- Katsina City News
- 13 Jan, 2025
- 444
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) reshen Kano sun kama jami’ai biyar na Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Katsina bisa zargin karkatar da naira biliyan daya da miliyan dari biyu da casa’in da hudu, dubu dari uku da talatin da bakwai, dari shida da saba’in da shida, da kobo hamsin da uku (N1,294,337,676.53) mallakin gwamnatin jihar Katsina.
Wadanda aka kama sun hada da Rabiu Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim M. Kofar Soro, Ibrahim Aliyu da kuma Nura Lawal Kofar Sauri.
An kama su ne bayan samun korafi daga gwamnatin jihar Katsina wanda ke zargin cewa wadanda ake zargin sun yi wata hada-hada tare da karkatar da kudaden da suka kai N1,294,337,676.53 da aka ware wa jihar daga kungiyoyin duniya kamar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Medicins Sans Frontiers, da Alliance for International Medical Action (ALIMA).
Bincike na farko da hukumar EFCC ta gudanar ya gano cewa Rabiu Abdullahi, tsohon Daraktan Tara Kudade kuma yanzu Sakatare na Dindindin na Hukumar, ya amince da bude asusun banki da aka sanya wa suna "BOIRS" a bankin Sterling. Ya nada Sanusi Mohammed Yaro, Daraktan Asusun Kudade, da Ibrahim M. Kofar Soro a matsayin wadanda ke da damar sa hannu kan asusun. Bayan haka, an yi amfani da wannan asusu wajen karkatar da kudaden zuwa ga babban mai cin gajiyar kudaden, NADIKKO General Suppliers, wata kamfani mallakin Nura Lawal Kofar Sauri, mataimakin darakta a bangaren horarwa da jin dadin ma’aikata na hukumar.
Bincike ya kuma gano cewa Nura Lawal da kamfaninsa "NADIKKO" ne suka zama hanyoyin karkatar da kudaden da aka sace. An gano cewa an tura wadannan kudade zuwa asusun bankuna daban-daban mallakin wadanda ake zargi.
A halin yanzu, wadanda ake zargin suna tsare a ofishin hukumar EFCC reshen Kano. Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.