SANARWAR MANEMA LABARAI DAGA KUNGIYAR MURYAR TALAKA TA NAJERIYA. RANA:LITININ, 13 -01-2025
- Katsina City News
- 13 Jan, 2025
- 50
Kungiyar Muryar Talaka na jan hankalin 'yan Najeriya da su fahimci cewa mulkin Dimokaradiyya ya fi mulkin kama-karya, domin shi ne, ke ba 'yan kasa dama su zabi wakilansu,wadanda za su aiwatar masu da dokoki da tsare-tsaren da za su magance masu matsalolin dake addabar su.
Ana gudanar da mulkin Dimokaradiyya bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki,wanda al'umma suka rubuta da kan su.
A karkashin tsarin mulkin Dimokaradiyya, 'yan Najeriya na da 'yanci,kamar 'yancin rayuwa, 'yancin fadin albarkacin baki, 'yancin zabe ko yin takara, 'yancin samun adalci a shari'a, da sauran damarmaki da muke dauka kamar ba komai ba ne.
Daga shekarar 1999 zuwa yau, 'yan Najeriya suna ci gaba da cin moriyar mulkin Dimokaradiyya a bangarori da dama kama daga fannin tattalin arziki,zuwa kiwon lafiya, ilmi, hanyoyi, inganta noma da kiwo,da sauran dimbin ababen more rayuwa.
A bayyane take cewa wasu 'yan Najeriya sun manta irin bakar ukubar da suka Sha a zamanin mulkin soja.
A duk lokacin da aka yi juyin mulki , ana dakile ma 'yan kasa 'yancin fadin albarkacin baki, 'yancin 'yan jarida.
An kulle mutane da yawa a gidajen kaso ba tare da an ba su damar samun lauyan da zai kare su ba.
An halaka mutane da dama ba tare da an yi masu shari'a ba.
Don haka, muna jinjina ma gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar ECOWAS, saboda amfani da hanyoyin difilomasiyya don sasanta sabanin dake tsakanin su da gwamnatocin mulkin soja na Burkina Faso, Mali da Janhoriyar Nijar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu,ya tura kwamiti mai karfi da ya kunshi tsohon shugaban kasa, sarakuna, da mallaman addini zuwa kasar Nijar domin a sasanta.
Kazalika, muna yaba ma shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa kokarin da yai na janye Nijar, takunkumin , kungiyar ECOWAS, da Kuma , kokarin da ya ke na ganin sojoji sun mayar da mulki ga farar hula tare da sakin shugaba Bazoum Mohammed.
Sannan muna jinjina game da kokarin da ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar wajen amfani da difilomasiyya don warware matsalar Nijar, Mali da Burkina Faso,da Kuma kokarin maido da mulkin farar hula.
Daga karshe, muna kira da gwamnatin Najeriya, ta kara himma wajen karfafa tsarin Dimokaradiyya,inganta zabe,da tuntubar al'umma.
Allah ya ja zamanin Najeriya.
Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi,
Shugaban Kungiyar Muryar Talaka ta kasa.
Kwamred Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta kasa.