SAMAR DA TSARO: GWAMNATIN ZAMFARA TA YABA WA SOJOJIN SAMA, TA KUMA JAJANTA WA AL'UMMAR DA HARIN JIRGIN SOJI YA SHAFA
- Katsina City News
- 12 Jan, 2025
- 161
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba da ƙoƙarin da sojojin Nijeriya ke yi na kai hare-hare kan ’yan bindiga ba ƙaƙƙautawa a jihar.
A ƙarshen makon da ya gabata ne rundunar sojin saman Nijeriya ta kai wani samame kan ’yan bindigar da ke yunƙurin kai hari a ƙauyukan ƙananan hukumomin Zurmi da Maradun.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Gusau, kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya jajanta wa iyalan fararen hula da harin da jirgin sama ya rutsa da su a Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Zurmi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, fararen hular da suka rasa rayukansu ’yan sintiri ne na yankin da aka yi zaton cewa ‘yan bindigar da suka tsere ne daga Gidan Makera a gundumar Boko a ƙaramar hukumar Zurmi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mun samu rahotanni masu inganci da yawa na farmakin da rundunar sojin sama ta Operation Fansar Yamma ta kai a ƙarshen mako a ƙananan hukumomin Maradun da Zurmi da ke fama da rikicin ’yan bindiga.
“Wannan farmakin da sojoji suke kaiwa ya rage wa ‘yan bindigar ƙwarin gwiwa matuƙa, ya kuma nuna aniyar rundunar sojojin saman Nijeriya na gudanar da aikin da Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ya ba su na kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
“A matsayinmu na gwamnati mai kishin ƙasa, muna tabbatar wa ɗaukacin al’ummar jihar cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ci gaba da samun nasarori a yaƙi da ’yan bindiga. Nasarar da aka samu a baya-bayan nan na nuni da cewa ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na jiha da na tarayya ya haifar da sakamako mai kyau.
“A bisa waɗannan nasarorin da aka samu, gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyar ta na bayar da dukkanin tallafin da ya kamata ga rundunar sojin saman Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin ci gaba da gudanar da ayyukansu da kuma samar da zaman lafiya mai gorewa a jihar.
“Za mu ci gaba da ba da tallafi don inganta musayar bayanan sirri, samar da dabaru, da kuma ƙarfafa cuɗanyar da jama’a da jami'an tsaro, duk a bisa tsarin da ya dace na tabbatar da tsaro da kuma cimma burin maido da zaman lafiya a dukkan sassan jihar.
“Abin takaici, harin ya shafi wasu ’yan sintiri (JTF) a yayin farmakin a Tungar Kara, wanda ya yi sanadin asarar rayuka. Muna roƙon Allah Ta'ala ya saka musu da gidan Aljannah.
“Gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyyarta ga iyalan jami’an JTF da suka mutu tare da ba su tabbacin cewa sadaukarwar da mamatan suka yi ba zai tafi a banza ba. Gwamnati za ta ba da tallafi da taimakon da ya dace ga iyalan waɗanda suka rasu.
“A ƙarshe, gwamnati na kira ga jama’a da su lura, su kai rahoton duk wani motsin da ba su gane masa ba, sannan su ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai. Ta hanyar haɗin kai za a iya samun nasarar yaƙi da ‘yan bindiga tare da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Zamfara.”