Wane Lokaci Ne Mafi Dacewa Domin Atisayen Rage Ƙiba?
- Katsina City News
- 12 Jan, 2025
- 87
Atisaye tare da tsara cimaka sune hanyoyin rage ƙiba mafiya tasiri, waɗanda kuma ba su da wani lahani ga jiki. Sai dai, game da atisaye, akwai ruɗani kan wane lokaci ne mafi dacewa domin yin atisayen.
Mafi yawan bincike da kuma ra'ayoyin masana kan atisayen rage ƙiba sun karkata zuwa zaɓar lokacin safe kafin karyawa domin yin atisayen rage ƙiba, saɓanin lokutan rana ko yamma.
Daga cikin dalilan zaɓar safe sun haɗa da cewa:
1. Idan mutum ya yi baccin awa 6 zuwa 8, to a lokacin da mutum ya tashi daga baccin kamar ya yi azumin cin abinci ne na aƙalla awa 6 zuwa 8. Saboda haka, yawan siga(gulukos) da ke cikin jininsa da safe ba shi da yawa, saboda haka, da zarar ya fara atisaye jiki zai ƙone shi. Bayan jiki ya ƙone ɗan ragowar gulukos ɗin da ke cikin jini, domin cigaba da atisayen, dole jiki ya fara tatso kitse daga sassan jiki tare da sarrafa shi zuwa gulukos domin cigaba da atisaye. Shi kuwa ƙone kitse yayin atisaye shi ne jigon atisayen rage ƙiba.
2. Hakan nan, ana ganin safiya lokaci ne da ke da sauƙin ayyuka da uzurai. Mutum zai iya yin atisayensa kafin fara uzuransa
na ranar. Kuma lokaci ne da zai fi taimaka wa mutum ɗorewa da atisayen.
Sai dai, duk da haka, abu mafi tasiri wajen rage ƙiba shi ne jurewa da ɗorewar atisayen akai-akai tsawon lokaci.
To yaushe za a fara ganin tasirin atisayen rage ƙiba?
Atisayen rage ƙiba na aƙalla minti 30 zuwa 60 a rana, sannan sau 3 zuwa 4 a sati, tsawon sati 6 zuwa 7, shi ne ake sa ran za a fara ganin tasirin atisayen a jiki.
Daga ƙarshe, kiyayi kasadar fara atisaye ba tare da tuntuɓar kwararru ba.
© Physiotherapy Hausa