Taron Cikar Jaridar Almizan Shekaru 35: Muhimman Jawabai Akan Aikin Jarida
- Katsina City News
- 12 Jan, 2025
- 19
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2025, an gudanar da gagarumin taron tunawa da cikar jaridar Almizan shekaru 35 da kafuwa. Taron ya gudana a babban dakin taro na Mambayya House da ke Kano, inda aka samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Najeriya, da kuma wakilai daga kasashen ketare, wanda hakan ya nuna muhimmancin wannan jarida wajen yada labarai da habaka ilimi cikin gaskiya da adalci.
An gudanar da muhawara da lakcoci masu muhimmanci akan nau’o’in aikin jarida, musamman investigative journalism (bincike na musamman), wanda ke da matukar tasiri wajen bankado gaskiya da bayar da labarai masu inganci ga jama’a.
Malam Ibrahim Musa, Editan jaridar Almizan, ya gabatar da wani gagarumin jawabi mai taken “Jaridar Almizan: Daga Inda Aka Fara, Inda Aka Kai, da Inda Aka Nufa.” Ya bayyana irin gwagwarmayar da jaridar ta sha wajen tsayawa kan gaskiya da kare muradun al’umma.
Babban jawabin taron ya fito daga bakin Malam Naziru Mikailu, tsohon babban edita a gidan rediyon BBC Hausa, wanda ya yaba wa jaridar Almizan bisa gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen bunkasa harshen Hausa da yada labarai cikin gaskiya. Ya ce, "Almizan ta zamo ginshikin aikin jarida a Najeriya, musamman a fagen harshen Hausa."
Fitaccin manyan baki sun hada da:
- Farfesa Mohammad Israr, Mataimakin Shugaban Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN).
- Barista Haruna Magashi, lauya kuma masani a fannin shari’a.
- Honorabul Abdullahi Usman Tumburkai, dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Dandume a karkashin PDP.
- Muhammad Danjuma Katsina, babban edita na jaridar Katsina Times.
Bugu da kari, taron ya samu halartar wakilai daga jihohin Katsina, Kano, Jigawa, Zamfara, Bauchi, Yobe, da birnin tarayya Abuja. Wakilai daga kasashen ketare kamar Nijar, Kamaru, Chadi, da Ghana sun halarta, suna mai jaddada alakar kasa da kasa da jaridar Almizan ke karfafa.
Taron ya kuma ba da dama ga mahalarta su tattauna hanyoyin amfani da aikin jarida don ci gaban al’umma. An yi kira ga ’yan jarida su kasance masu bin ka’idojin aiki, su tsayu kan gaskiya da adalci.
Taron cikar jaridar Almizan shekaru 35 ya kasance wani babban tarihi da aka kulla, inda aka jaddada muhimmancin aikin jarida wajen tabbatar da ci gaban al’umma. Mahalarta taron sun jaddada muhimmancin ci gaba da yin aiki tukuru don tabbatar da cigaban harshe da al’umma baki daya.