Kwamandan Rundunar Soja Ta 17, Birgediya Janar Bo Omopariola, Ya Bayyana Muhimman Saƙonni Ga 'Yan Jarida a Katsina
- Katsina City News
- 10 Jan, 2025
- 32
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A yayin wata tattaunawa ta musamman tare da Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da sojojin Najeriya, a ranar Juma’a 10 ga Janairu, 2025, a Natsinta Barracks, Katsina, Kwamandan Rundunar Soja ta 17, Birgediya Janar Bo Omopariola, ya jaddada niyyar sojoji wajen inganta alaƙa da 'yan jarida da kuma inganta watsa labarai a kan lokaci.
Da yake jawabi a taron, Omopariola ya amsa tambayoyi daga wakilan jaridu daban-daban inda ya yi ƙoƙarin fayyace batutuwan da suka shafi yadda bayanai ke tasowa daga hedkwatar tsaro. Ya ce, “Tsarin watsa labarai na sojoji ya ginu ne daga sama zuwa ƙasa, domin tabbatar da cewa ana watsa labarai ba tare da ragi ko kuskure ba."
Ya bayyana cewa, duk da tsarin watsa labarai daga hedkwatar tsaro, rundunarsa za ta tabbatar da cewa ana ba wa 'yan jarida bayanai cikin gaggawa da zarar an fitar da su daga hedkwatar tsaro. "Za mu tabbatar cewa APR ɗinmu zai isar da bayanan cikin awa guda bayan an fitar da su," in ji shi.
Dangane da karancin damarmaki ga kafofin watsa labarai na Hausa, Birgediya Janar Omopariola ya ce, "Za mu kara ba wa kafofin watsa labarai na Hausa kulawa, musamman saboda muhimmancin da suke da shi wajen isar da saƙonni ga jama’a." Ya kuma nuna ƙudurin su na haɗa wakilan kafofin watsa labarai na Hausa cikin ayyuka da rahotanni na musamman.
Kwamandan ya tabbatar wa wakilan jaridun cewa daga wannan lokaci ba za a sake yin watsi da kiran su ko tambayoyinsu ba. Ya ce, “Za mu tabbatar da cewa an amsa kiran ku, ko da kuwa ba mu da cikakkun bayanai a lokacin, za a sanar da ku a kan lokaci."
Janar Omopariola ya yi kira ga 'yan jarida da su tabbatar da bincike mai zurfi kafin fitar da labarai. Ya ce, "Yana daga cikin dalilin wannan ganawa mu sauƙaƙe hanyar sadarwa da inganta fahimta tsakanin sojoji da 'yan jarida."
Kwamandan ya sanar da kafa wani dandali ta WhatsApp don inganta sadarwa tsakanin sojoji da 'yan jarida. Wannan dandali, in ji shi, zai haɗa jami’an hulɗa da jama’a, da ma'aikatan ayyuka da sadarwa domin watsa labarai cikin gaggawa.
Ya jaddada cewa tsaron 'yan jarida yana da matuƙar muhimmanci, musamman idan aka kawo batun ziyarar sansanoni da yankunan da ake fama da rikici. Ya ce, "Ba za mu yi kasadar kai ku inda ba za mu iya tabbatar da lafiyarku ba."
Da yake magana a madadin Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Shugaban reshen jihar Katsina, Malam Tukur Hassan Danali, ya yabawa rundunar sojoji bisa wannan ci gaban. Ya ce, “Wannan tattaunawa ce da za ta cusa wani sabon salo a dangantakar tsakanin sojoji da 'yan jarida, musamman ma wajen samun bayanai cikin gaggawa da kuma inganta fahimtar juna."
Ya ƙara da cewa, "NUJ za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tabbatar da cewa labaran da muke bayarwa sun dogara ne akan gaskiya da bincike mai zurfi. Muna sa ran wannan haɗin gwiwa zai haifar da da mai ido ga dukkan ɓangarori."
Taron ya kasance babbar dama ta musayar ra'ayoyi da kuma ƙirƙirar wani sabon tsari na sadarwa da zai inganta dangantaka tsakanin jami'an tsaro da 'yan jarida, tare da tabbatar da cewa jama’a sun sami sahihan labarai akan lokaci.